قَوْلُهُ عَلَيْهِ السَّلَامُ مُقَدَّمٌ عَلَى أَقْوَالِ النَّاسِ
Fassara:
“Maganar Manzon Allah (S.A.W) ita ake gabatarwa a kan magana mutane baki ɗaya “ Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/7].
Fashin Baƙi:
Wannan magana ta babban malami Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama ƙa’ida ce da tushenta yake da dalilai daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma malamai da dama sun jaddada muhimmancinta da wajabcin aiki da ita a fili da ɓoye.
Allah Ta’ala Yana cewa:” Ya ku mummunai! Ku yu ɗa’a ga Allah, kuma ku yi ɗa’a ga Manzo da kuma majiɓinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar ƙarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyawun makoma” Suratun Nisã’i aya ta 59.
Wannan aya tana nuna cewa idan aka sami saɓani, to dole ne a mayar da al’amari zuwa ga Allah da Manzonsa, wato Alƙur’ani da Sunna. Allah Ta’ala Ya ƙara cewa:” Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karɓe shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah, Lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.” Suratul Hashri aya ta 7. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk abin da na hane ku, to ku nisance shi; kuma abin da na umarce ku, to ku aikata shi gwargwadon iyawarku.” Bukhari ne ya ruwaito [#7288] da Muslim[#1337]. Wannan hadisi yana nuna cewa dole ne a bi umurnin Annabi (S.A.W) kuma a nisanci abin da ya hana.
Maganganun Malamai:
Banyan malaman Musulunci kuma jagorin shiriya sun bayyana maganar Manzon Rahama(S.A.W) ita ce ta fi cancanta abi a kan maganar mutane baki ɗaya. Ga maganar wasu daga cikinsu:
Imam Abu Hanifa Allah Ya yi masa rahama yana cewa:” Idan hadisi ya inganta, to shi ne Mazahabata” Duba Ibnu Abidin; al-Hãshiyatu [1/63]. Wannan yana nuna cewa Imam Abu Hanifa yana fifita hadisin Annabi (S.A.W) kan ra’ayinsa ko ijtihadinsa.
Imam Malik Allah Ya yi masa rahama shi kuma cewa ya yi:” Ni mutum ne, ina yin daidai kuma ina kuskure, ku duba ra’ayina, duk wanda ya dace da Alƙur’ani da Sunna, to ku riƙe shi, duk kuma wanda ya saɓa wa Alƙur’ani da Sunna, to ku bar shi.” Duba Ibnu Abdilbarri; Jãmi’u Bayãnil ilmi [2/32]. Imam Malik yana nuni da Alƙur’ani da Sunnar Annabi (S.A.W) su ne abin gabatarwa a bisa maganarsa.
Imam ash-Shafi’i Allah Ya yi masa rahama shi kuma cewa ya yi:”Idan hadisi ya inganta, to shi ne Mazahabata” Duba an-Nawawi; al-Majmū’u [1/63]. Wannan yana nuna cewa Imam ash- Shafi’i yana fifita hadisin Annabi a kan ra’ayinsa ko ijtihadinsa.
Imam Ahmad ɗan Hanbal Allah Ya yi masa rahama cewa ya yi:” Duk wanda ya ƙi karɓar Hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, to yana gaɓar halaka” Duba Ibnul Jauzi; al-Manãƙibu [shafi na 182].
Wannan yana nuna cewa Imam Ahmad yana karɓar koyarwar Annabi (S.A.W) fiye da ra’ayoyin mutane, kuma ƙin karɓar hadisi halaka ne.
Maganar Ibn Juzai tana tabbatar da cewa maganar Annabi Muhammad (S.A.W) ita ce ake ba wa muhimmanci a kan maganar sauran mutane, kuma ita ce shiriya, saɓa mata kuma halaka ne da ɓata. Allah Ya datar da mu da bin Annabi (S.A.W) a fai da ɓoye. Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp