“التَّقْوَى مَصْدَرٌ مُشْتَقٌّ مِنَ الوِقَايَةِ، مَعْنَاهَا الخَوْفُ وَالِالْتِزَامُ بِطَاعَةِ اللهِ وَتَرْكُ مَعَاصِيهِ، فَهِيَ جَامِعَةٌ لِكُلِّ خَيْرٍ”
Fassara:
“Takawa kalma ce da aka samo daga ‘kariya’ Ma’anar taƙawa shi ne jin tsoron Allah, da lazimtar biyayya ga Allah da barin saɓa Masa. Taƙawa ta tattaro dukan alherai gaba ɗaya. “ Duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzil [1/17]
Fashin Baƙi:
Maganar babban malami Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, tana bayyana ma’anar taƙawa a harshen Larabci, da kuma harshe na na shari’a.
Taƙawa a harshen Larabci: tana nufin ‘kariya’. Attaƙawa (التَّقْوَى) ta samo asali daga wiƙãya (وِقَايَة), wacce ke nufin katanga ko kariya. Wannan yana nuna cewa taƙawa tana nufin kare bawa daga azabar Allah ta hanyar bin umarninsa da guje wa saɓonsa.
Ma’anar Taƙawa a Shari’a: Ibnu Juzai al-Kalbi ya fassara taƙawa da jin tsoron Allah da lazimtar biyayya gare shi da barin saɓa masa. Wannan yana daidai da abin da malamai kamar Ibn Rajab da al-Gazzali suka bayyana, cewa taƙawa ba wai tsoro kaɗai ba ne, har da tsoron da ke haddasa aiki da biyayya.
Jin tsoron Allah: Wannan yana nufin mutum ya san Allah da girmansa, wanda hakan ke sa shi jin tsoron yin abin da zai jawo fushinsa.
Lazimtar biyayya: Wato mutum yana da nufin aikata duk abin da Allahda Manzonsa suka yi umurni da shi.
Barin saɓo: Wato mutum yana nisantar duk wani abu da zai jawo fushin Allah na magana ko aiki, na fili da na ɓoye.
Faidojin Taƙawa:
Taƙawa tana da fa’idoji masu yawa, da suka haɗa da: Samun ƙauna daga Allah da kankarar zunubai da girmama lada da mutum zai samu. Taƙawa sababi ce ta samun albarkatun Allah, da toshe kofofin sharri.
Taƙawa tana sanya mutum ya sami mafita a rayuwarsa duk rintsin da mutum zai shiga. Taƙawa tana sanya al’amuran bawa su zama masu sauƙi. Taƙawa tana sanya mutum ya sami rabauta da rahamar Allah, tana kuma sanya mutum ya sami tsira.
Taƙawa tana sanya mutum ya girmama Allah da kuma sanya mutum ya zama adali mai nagarta a cikin al’umma, sannan tana sanya mutum ya nisanci zalunci tare da lazimtar gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp