درجاتُ التَّقوى خمسٌ: أنْ يَتَّقِيَ العبدُ الكفرَ، وهو مقامُ الإسلامِ، وأنْ يَتَّقِيَ المعاصيَ والحرماتِ، وهو مقامُ التَّوبةِ، وأنْ يَتَّقِيَ الشُّبُهاتِ، وهو مقامُ الوَرَعِ، وأنْ يَتَّقِيَ المُباحاتِ، وهو مقامُ الزُّهدِ، وأنْ يَتَّقِيَ حضورَ غيرِ اللهِ على قلبِهِ، وهو مقامُ المُشاهدةِ.
Fassara:
“ Matakan taƙawa guda biyar ne: kare kai daga kafirci; Wannan shi ne matakin Musulunci. Kare kai daga aikata sɓon Allah da haram; Wannan shi ne matakin tuba. Kare kai daga shubuha; Wannan shi ne matakj na tsantseni. Kare kai daga abubuwan da aka halatta; Wannan shi ne matakin gudun duniya. Kare zuciya daga duk wani abu da ba Allah ba; Wannan shi ne matakin bautar Allah kamar kana ganin Sa.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/36]
Fashin Baƙi:
Wannan magana ta Ibn Juzai al-Kalbi tana bayani ne kan matakan da mutum zai bi domin kaiwa ga matakin taƙawa na ƙoli, daga mafi ƙasa zuwa mafi girma. Bari mu yi nazari da sharhi akan kowanne mataki daga cikinsu:
Mataki na Ɗaya: Kare kai daga kafirci; wato matakin Musulunci, wannan matakin yana nufin cewa musulunci shi ne matakin farko na taƙawa. Duk wanda zai zama mai taƙawa, dole ne ya fara da tabbatar da imani ga Allah, ya yarda da Manzonsa (SAW), kuma ya kauce wa duk wani nau’in kafirci. Wannan yana nufin mutum ya ƙudurce kalmar shahada tare da furta ta da kuma aiki da ita. Ya shaida shahada, wanda ita ce tushen addini. Idan babu wannan, to, duk wani ƙoƙari da mutum zai yi a kan taƙawa ba zai amfane shi ba.
Mataki na Biyu: Kare kai daga aikata saɓon Allah da aikata haram, wato matakin tuba; wannan matakin yana bayani ne akan wajabcin nisantar haram da kuma tuba daga zunubi. Idan mutum ya tabbatar da imani, mataki na gaba shi ne ya kiyaye dokokin Allah ta hanyar kauce wa haram. Duk wanda bai nisanci abin da Allah ya haramta ba, yana nuna gazawarsa a cikin taƙawa. Wannan matakin yana bayyana cewa taƙawa ba kawai a zuciya take ba, sai an aiwatar da ita a aikace.
Mataki na Uku: Kare kai daga shubuha; wato matakin tsantseni, shubuha na nufin abubuwan da ba a tabbatar da halacci ko haramcinsu ba. Akwai wani mataki da ya fi kauce wa haram, wato kauce wa abubuwan da ke da shakku. Annabi (SAW) ya ce:
” Lalle halal a bayyane take, kuma lalle haram a bayyane yake, amma akwai wasu abubuwa masu rikitarwa a tsakanin su waɗanda mutane da yawa ba su san su ba, wanda ya nisanci shubuha, to ya kare addininsa da mutuncinsa.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Saboda haka, matakin tsantseni yana nufin mutum ya kiyaye kansa daga duk wani abu da zai iya kai shi ga haram, koda kuwa ba a tabbatar da haramcinsa ba.
Mataki na Huɗu: Kare kai daga abubuwan da aka halatta; wato matakin gudun duniya. Wannan matakin ya fi zurfi domin yana nuni da zuhudu (wato yin watsi da son duniya). Duk da cewa akwai halal da aka ba wa mutum damar amfani da su, sai dai matakin mafi girman taƙawa shi ne rage kwaɗayin duniya domin kauce wa duk wani abu da zai shagaltar da mutum daga bautar Allah. Wannan ya dace da hadisin Annabi (SAW) da ya ce: “Ka kasance a duniya kamar baƙo, ko kuma kamar wani matafiyi.” Bukhari ne ya ruwaito. Don haka, matakin gudun duniya yana nuna cewa taƙawa ta gaskiya ba kawai da nisantar haram ba ce, har ma da rage dogaro da duniya don samun kyakkyawan sakamako a lahira.
Mataki na Biyar: Kare zuciya daga duk wani abu da ba Allah ba. Wato matakin bautar Allah kamar kana ganin Sa. Wannan shi ne matakin ihsani wanda Annabi (SAW) ya bayyana a hadisin Jibrilu da cewa:
“Ihsan shi ne ka bauta wa Allah kamar kana ganin Sa, idan ba ka ganin Sa, to Shi yana ganin ka.” Muslim ne ya ruwaito. Wannan matakin yana nuna tsarkake zuciya daga kowanne abu da zai shagaltar da mutum daga Allah. Ana son mai taƙawa ya kasance zuciyarsa a koyaushe a tare da Allah, yana ƙaunar Sa fiye da komai. Wannan matakin ne mafi girma a taƙawa, domin yana nuni da mutum ya kasance kullum yana jin tsoron Allah tare da ƙaunar Sa, ba wai kawai yana gudun azabarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp