An bayyana cewar gudanar da adduoi na musamman a kowanne lokaci shi ne yake kawo saukin faruwar kowanne irin nau’in miyagun ayyuka a kowacce kasa ce a karshe ma aka ce addu’a ita ce ginshikin kare dukkan wani bala’i da ke iya fadowa kasa ko kuma al’ummar cikin kasar baki daya.
Alhaji Bature Karaye Kuma Falakin Karaye mazaunin Legas yana daya daga cikin masu gudanar da irin wadannan adduo’i, inda a makon jiya ya shirya irin wadannan tarurrukan na gudanar da adduo’i inda ya shirya taron gudanar da adduoin guda biyu addu’ar neman karin samun zaman lafiya a Nijeriya da kuma addu’ar daura masa aure da amaryarsa a Kanon Dabo taron gudanar da addu’oin guda biyu wanda ya gudana a masallacin marigayi shiekh Malam Ja’afar Adam da ke unguwar dorayi a cikin garin Kano.
- Kidayar ‘Yan Nijeriya Ta 2023: Shugaba Buhari Zai Bude Taron Masu Ruwa Da Tsaki
- Tsadar Man Dizil Na Barazana Ga Masu Kiwon Tarwada A Edo
Taron addu’oin guda biyu wanda ya kunshi malamai magada annabawa da kuma wadansu daga cikin shugabannin kasuwar mile 12 intanashinal market da ke cikin birnin Legas wanda suka hada da shugaban majalisar dattawan kasuwar, Alhaji Isa Mohammed Mai Shinkafa da tsohon shugaban kasuwar ta mile 12 Alhaji Haruna Mohammed Tamarke.
Mai Dankalin turawa da Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki sauran sun hada da Abdulwahab Tsoho Babangida da babban shugaba mai kulawa da cigaban kasuwancin tumatur a Legas Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano da Alhaji Sabo Magaji Karaye daya daga cikin abokan Alhaji Bature Karaye da sauran wadansu shugabannin bangarorin kasuwar baki daya.