An so idan akwai hali, mai ziyara ya yi kwana takwas a Madina yana gabatar da sallolin farillan nan guda biyar tare da Annabi (SAW) a Masallacinsa. Ma’ana mutum yana sallah ga kuma Annabi (SAW) a Masallacin.Â
Idan kuma Hukumar Alhazai ba ta bari ba, shikenan. Ko na kwana daya mutum ya yi da Annabi (SAW) ya isa dukkan falala.
- An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla
- Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG
Dole ne ko wane Musulmin Kwarai ya girmama Manzon Allah (SAW) ya daraja shi tare da bin sa.
A cikin Alkur’ani maigirma Allah (SWT) ya ce, “Mu muka aiko ka – ya Rasulallahi a matsayin – maishaida, maibishara, maigargadi (ga al’ummarka), – ku kuma al’ummarsa – ku yi imani da Allah, da Manzonsa, ku daraja shi, ku kai matukar girma wurin daraja shi.”
Malam Mubarridu ya ce ma’anar “wa tu’azziruhu” a cikin ayar ita ce “ku kai matuka cikin girmama Manzon Allah (SAW).
Don haka Musulmi kar su yarda wani ya rude su ya yi musu dodorido idan an ga suna girmama Annabi (SAW) a ce musu ‘yan bid’ah sai su ji shakka su daina. Da irin wannan fahimtar ce aka je aka tada wa Annabi (SAW) bom a Masallacinsa.
Hatta Sahabban Annabi (SAW) sun fuskanci irin haka, babu abin da ba a fada musu ba, an ce musu wawaye saboda sun yi imani kuma duk abin da Manzon Allah (SAW) ya ce su yi ba sai sun tambaya ba, kawai yi suke.
Malamai sun bayyana cewa girmama Manzon Allah (SAW) bayan rasuwarsa, daidai yake da girmama shi kamar lokacin da yake da rai, babu banbanci. Kamar yadda ka san idan ka je gabansa yana raye za ka yi ladabi, haka ma yanzu idan ka je kabarinsa.
Yana daga girmama Manzon Allah (SAW) idan za ka ambaci sunansa, kar ka yi kamar na sauran mutane, ka sanya ladabi da natsuwa. Shi ya sa galibi masoyansa suka fi kiran mutanen da aka sanya musu sunansa (SAW) da lakabi. Maimakon Muhammadu, sai a rika fadar lakabin Nura, Hadi, Amin, Kamal, Nazir, Kamil da sauran su. Sannan da an ambaci sunan ka yi ma sa salati.
Haka nan yana daga girmama shi (SAW), idan mutum zai karanta Hadisinsa, ya yi shiga mai kyau tare da natsuwa da kankantar da kai. Haka nan ya girmama Sunnarsa.
Ma’anar Sunnah ita ce abin da Annabi (SAW) ya yi ko ya umurci a yi ko kuma aka yi a gabansa bai hana ba. Amma ba kamar yadda wasu ke dauka ba musamman a kwanan nan, raina Allah da Manzonsa da wulakanta darajojin iyalan gidan Annabi (SAW) da sahabbansa a matsayin Sunnah.
Yana daga girmama Manzon Allah (SAW) da son sa, mutum ya rika shaukin jin tarihinsa da girmama iyalan gidansa da sahabbansa da malaman Musulunci magada Annabawa da duk wani abu da ya rataya da shi (SAW). Tun daga kan garin da ya zauna a ciki, da gidansa, da kayan da ya yi amfani da su har ma da ire-iren abincin da ya fi so da suturar sawa, duk a so su, a ga girmansu, ballantana kuma kabarinsa
Ya zo cikin Hadisi madaukaki cewa “Mumini ana binne shi ne a kasar da aka gina shi da ita.” Ma’ana duk inda aka binne mutum, da kasar wurin ne aka kwaba aka yi halittarsa da ita.
Kenan kasar Madina tana da matukar girma, don da ita ce aka gina Manzon Allah (SAW) da ita. Koda yake za a iya cewa ta yaya aka haife shi a Makka ba a Madina ba? To Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito Hadisin da cewa “lokacin da aka yi ruwan dufana ne Allah ya tafiyar da kasar halittarsa (SAW) zuwa Makka.”
Saboda haka kamar yadda Annabi (SAW) ya kasance mafificin Dan Adam, to kasar da aka yi halittarsa da ita ita ce mafificiyar kasa. Kuma shi ya sa Manzon Allah (SAW) ya ce “Ba domin yin Hijira – don Zatin Allah – ba (daga Makka zuwa Madina) da a Madina ma aka haife ni”. Tirmizi ya ruwaito Hadisin.
Domin fitar da abin a fili ma, Kakar-Kakar Manzon Allah (SAW) Salma’a wadda ta auri Hashimu ‘yar Madina ce daga kabilar Banin Najjar. Haka nan don Allah ya nuna wa mutane lamarin, sai Mahaifinsa Sayyidina Abdullahi (RA) ya zo ya rasu a Madina a lokacin da ya ziyarci dangin Kakarsa Salma’a. A da akwai gidan da ake zuwa ana ziyarar kabarin Kafin Ahlu Sa’ud su kama Madina su rufe wurin.
Ita ma Mahaifiyarsa Sayyida Amina (RA) ta ziyarci mijinta, Baban Annabi (SAW) tare da shi, da Ummu Aimana, a kan hanyarta ta komawa daga Madina ta rasu a Ab’wa. Daga Madina zuwa Ab’wa kilomita 150 ne. Amma tsakanin wurin da Makka kilomita 250.
Ibn Baddalu ya ce “Kamshin Madina ya ninka na ko ina”. Imamu Malik (RA) ya yi fatawa a yi wa wani mutum da ya ce kasar Madina lalatacciya ce bulala 30 kuma a kulle shi a kurkuku. Sai aka ce ma sa wannan mutumin babba ne fa? Sai ya ce “Ai ba bulala ya dace a yi ma sa ba, a daki wuyarsa kawai.” Ma’ana a kashe shi.
Akwai sabani a kan wadda ta fi daraja tsakanin Makka da aka haife shi (SAW) da Madina wadda ya yi Hijira kuma ya rasu a can. Ko wacce akwai Sahabbai da Malamai da suka goyi bayan fifikonta. Amma a wurin mu Malikawa, Madina ta fi daraja.
Sannan da Malikawan da sauran malaman Maz’habobin duk sun yi ittifakin cewa nan Shabbakin Manzon Allah (SAW) da ke kunshe da jikinsa ya fi ko wane wuri a kan kasa. An ciro wannan ne daga Tajuddinis subki. Shi kuma ya sake cirowa daga Ibn Akilul Hambali cewa “Wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) ya fi har Al’arshi”.
Imamul Fakihani, ya ce “wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) ya fi sama ya fi kasa”. Haka nan, Alkadiy Iyad ya ce “Babu wani wurin da ya kai a hada shi da wurin da aka binne jikin Manzon Allah (SAW) saboda abu biyu: na farko, cewar da aka yi ko wane mutum ana binne shi a kasar da aka yi shi da ita, to nan wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) kasar jikinsa ne, to wane abu ne za a iya hada shi da jikinsa (SAW)? Na biyu, bisa irin Mala’ikun da suke sauka a nan wurin, da irin albarkar da take sauka, da salatin da ake aikawa da sauran alheran da ke sauka a wurin, babu wani wurin da ya kai shi.”
Abu Ya’ala ya ruwaito Hadisi daga Sayyidina Abubakar (RA) ya ce, ya ji Manzon Allah (SAW) ya ce “Allah ba ya karbar Annabinsa sai a wurin da Annabin ya fi so.” Sayyidina Abubakar ya fadi Hadisin ne lokacin da Annabi (SAW) ya yi wafati sa’ilin da aka samu sabani kan wuri mafi dacewa a binne shi (SAW). Saboda haka suka ce babu shakka wurin da Annabi (SAW) ya fi so, nan ne Allah ya fi so. Domin son sa, yana biye ne da son Allah (SWT).
Imamun Nabahani ya ce, “Ziyarar kabarin Annabi (SAW) ita ce mafi girman kusanci zuwa ga Allah, ita ce mafi kaunar da’a ga Allah, ita ce hanyar da mutum zai bi ya samu kololuwar daraja. Duk wanda ya butulce ya ce ba haka ba, ya tube igiyar Musulunci daga wuyarsa. Kuma ya saba wa Allah, ya saba wa Annabi (SAW), ya saba wa tarin jama’ar malaman Musulunci na Allah.”
Alkadiy Iyad ya ce “Ziyarar Annabi (SAW) Sunnah ce daga sunnonin da Musulmi suka gaje ta kuma wacce aka hadu a kanta, falala ce abar kwadaitarwa.”
Darakudni ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina cetona ya wajaba a kansa.” Har ila yau, Darakudnin ya ruwaito daga Hadisin Abdullahi bin Umar (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarce ni bayan rasuwata kamar ya ziyarce ni ne ina cikin rayuwata”.
Zainuddin ibnil Husainil Maragiyu ya ce “Ya wajaba ga Musulmi ya kudurta cewa ziyarar Manzon Allah (SAW) kusanci ce; ibada ce saboda wadancan Hadisan guda biyu. Da kuma fadin Allah a cikin Alkur’ani cewa “da al’ummarka za su zalunci kansu sai su zo ma su nemi gafarar Allah a wajenka, kai kuma ka nema masu gafara, za su samu Allah mai karbar tuba da jinkai ne”.
Malamin sai ya kara da cewa “Manzon Allah (SAW) ya nema mana gafara, abin da ya rage sai mu je wurinsa, idan muka je sai mu nemi gafarar a gabansa. Shikenan abubuwa guda uku sun cika – mun je wurinsa, mun nemi gafara, ya nema mana gafara.”
Don haka, Alhajin da ya je ziyara kafin Arfa ya riga ya samu gafara tun kafin ranar Arfa sai ya zama garabasa biyu. Wanda kuma ya je bayan Arfa, abin da ya rage na daga zunubinsa da ya yi kafin zuwa ziyarar sai ya nemi gafarar a gaban Manzon Allah (SAW).
Ana so mai ziyara ya lizimci ladabi da kankar da kai, ya sunkuyar da ganinsa a yayin da yake ziyarar Annabi (SAW). Ya ji a ransa cewa ya zo wurin Annabi (SAW) kuma ga shi nan kamar yana ganinsa. Saboda babu banbanci tsakanin ziyararsa yana da rai da kuma bayan wafatinsa. Sannan mai ziyara ya rika tuna irin yadda su Sayyidina Abubakar (RA) suke ladabi a gabansa da magana a hankali. Kar mai ziyara ya yi kuru-kuru da ido, babu ladabi, babu natsuwa a tare da shi. Kar mutum ya kuskura ya bi maganganu wadanda suke raina janibinsa (SAW). Lamarin Annabi (SAW) ba na wasa ba ne, a kula da kyau.
Kuma ya kamata gwamnati ta kula da kyau, a rika samun jagororin mahajjata masu tsoron Allah da soyayyar Manzon Allah (SAW) don fadakar da Alhazai kan abin da ya fi zama daidai a Musulunci da Imani. Amma ba sharrori da munanan fahimta wanda da zarar mutum ya ji, ya san kiyayyar Manzon Allah (SAW) ce kawai ake koyar da mahajjata ba.
Hatta ita kanta Saudiyya yanzu abin ya dame ta, nema take ta gyara.
Akwai wasu da suke neman hana zuwa Madina ma kwata-kwata. Ko kuma su takura wa Alhazai a kan kar su yi kwana takwas din nan duk da cewa akwai Hadisi ingantacce kan haka.
Hadisin ba wai ya zo da adadin kwana takwas ne ba, amma yawan sallolin da Hadisin ya fada na adadin kwana takwas ne kamar yadda za mu kawo yanzu.
An karbo daga Anas bin Malik (RA), Annabi (SAW) ya ce “Duk wanda ya yi sallah a Masallacina guda arba’in ba tare da wata sallah ta tsere ma sa ba, za a rubuta ma sa takardar shaidar cewa ya kubuta daga wuta da duk wata azaba. Kuma zai kubuta daga munafunci.” Ahamdu bin Hambali ya ruwaito, shi ma Dabarani ya ruwaito da ingantaccen sanadi.
Idan aka buga lissafin sallolin farilla guda biyar da muke da su a rana, jimillar sallah 40 za ta zama ta kwana takwas.
Ya kamata a rika barin Alhazai suna samun wannan falalar. Abu ne da ya inganta a cikin Sunnar Annabi (SAW).
Kai ma mai ziyara ka san cewa ba hutu da shantakewa kawai za ka yi a Madina ba, ka yi kokari ikamar kowace sallah kar ta kubuce ma a Masallacin Annabi (SAW) idan ba akwai lalura mai karfin gaske ba.