• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Farar Dabarar Da Tsoffin Masana’antu Ke Yi A Kasar Sin Don Tafiya Da Zamani

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sin

Daya daga cikin abubuwan da nake tunani a kansu game da kasar Sin daga lokacin da na sa kafa a kasar shi ne, mece ce makomar masana’antu na tsohon yayi a kasar bisa sauyin zamani, shin ana rufe su ne ko ana mayar da su wasu abubuwa na daban? Dalilin wannan tunani shi ne yadda kasar ta rungumi zamanantarwa gadan-gadan a dukkan fannoni kuma a matakin koli. Ni dai a bisa fahimtar da na yi wa Sinawa, mutane ne da suka san darajar alkinta kayayyakinsu, don haka na san zai yi wahala a ce ana rufe wadannan tsoffin masana’antun saboda gibin da za su iya haifarwa na rashin aiki da kuma tattalin arziki. To amma kuma, me ake yi da su?

Ashe wata farar dabara ire-iren masana’antun suka runguma ta yadda suke shigar da zamani cikin ayyukansu tare da daga matsayinsu sakamakon tsare-tsaren da gwamnatin kasar ta samar musu. A cewar wasu bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin (MIIT), akwai masana’antu na karamin mataki da suke aiki da fasahohin zamani fiye da 30,000, da wadanda suke kan mataki mai zurfi guda 1,200 kana da wadanda suka kai matakin koli na gwanancewa 230 a kasar Sin.

  • ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 
  • Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan

Wadanda suke kan matakin na koli sun kasance a sassa daban-daban na lardunan kasar 31, da yankuna masu cin gashin kansu da manyan birane, sannan su ne suke da kaso 80 cikin dari na adadin kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki wadanda aka shigar da su sassan ayyuka kusan 2,000, ciki har da na gwajin aiki da fasahohin zamani, da zane-zanen kayayyaki a zamanance da kuma na matakin sarrafa kayayyaki.

Sakamakon tafiya da zamani, an samu raguwar matakan sarrafa kaya a ire-iren wadannan masana’antun da a kalla kashi 28.4 cikin dari, inda sauri da yawan ayyukan sarrafa kaya suka karu da kashi 22.3 cikin dari, kana aka samu raguwar lalacewar aiki da kaso 50.2, sannan bangaren fitar da hayaki mai gurbata muhalli ya ragu da kashi 20.4 cikin dari.

Misali daga wani kamfanin sarrafa karafa na HBIS Group Ltd wanda ya rungumi aiki da fasahar zamani hade da tsarinsa na tsohon yayi kamar yadda jami’in yada labarai na kamfanin, Li Xiaogang ya bayyana, a halin yanzu cikin mintuna 29 da dakika 7 kacal suke kera na’urar masarrafin karfe, inda aka samu raguwar lokacin da ake aikin da kashi 10 cikin dari, kana hayakin da ake fitarwa ya ragu da kashi 20 cikin dari.

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

A bangaren masaku ma, masakar Zhejiang Yingfeng ta samu bunkasar ayyukanta musamman wajen rage yawan abubuwan da ba a bukata domin fitar da kayan da ake sarrafawa da tsafta, bayan ta rungumi amfani da fasahar zamani. Haka nan bangaren rina kaya ya samu ci gaba da kusan kashi 80 zuwa 95 cikin dari.

Bangaren aikin gona shi ma yana samun habaka bisa amfani da fasahohin zamani wajen ayyukan noma, da kula da gonaki, da sayar da amfanin gona da sauransu. A garin Zhangzhuang dake gundumar Shangshui ta birnin Zhoukou dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, ana iya ganin yadda ake amfani da na’urori da fasahohin zamani a ayyukan gona a bangaren zuba taki da ban-ruwa, da taraktocin noma da jirage marasa matuka na shuka tsirrai. Kana manoma sun samu sauki sosai waje kula da gonaki ta amfani da manhajojin fasahar sadarwa.

Sashen gudanar da kasuwanci shi ma ba a bar shi a baya ba, inda a shekarar 2024, aka samu cinikin kaya ta manhajar sayar da kayayyaki ta zamani na kimanin yuan biliyan 23.5 a gundumar Ganyu ta birnin Lianyungang dake lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin.

Wadannan tsoffin masana’antun dai na ci gaba da samun bunkasa musamman wajen amfani da makamashi mara gurbata muhalli da fasahar sadarwar mai karfin 5G da kuma rungumar aiki da kirkirarriyar basira domin samun habaka daidai da juyin zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
Daga Birnin Sin

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

October 30, 2025
Next Post
Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan

Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

October 30, 2025
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 

October 30, 2025
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

October 30, 2025
Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

October 30, 2025
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

October 30, 2025
Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.