Ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta bayyana cewa farashin litar mai na iya sauƙa nan ba da jimawa ba, sakamakon farfaɗowar matatar man fetur ta Warri da kuma gasa a kasuwar mai.
Bincike ya nuna cewa a wasu gidajen mai a birnin Abuja, kamar Total, Azman, Conoil, da AYM Shafa, an samu ragin farashin litar mai daga Naira 1,020 zuwa Naira 965 a kwanakin baya-bayan nan.
- Rahoto: Sana’ar Watsa Labarai Ta Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Cudanyar Digital Da Basira
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Mikawa Juna Sakon Murnar Sabuwar Shekara
Wannan sauyi ya biyo bayan farfaɗowar matatar mai ta Warri, wanda aka ce yanzu tana tace dizal, kalanzir da nafta.
Babban jami’in IPMAN, Alhaji Zarma Mustapha, ya ce aikin matatar Warri da sabuwar matatar Fatakwal zai taimaka wajen rage tsadar mai tare da haɓaka wadatar mai a ƙasa.
Ya ƙara da cewa, a halin yanzu, gidajen man NNPC ne kawai ke samun dizal da kalanzir daga matatar Warri.
Shugaban NNPCL, Mallam Mele Kyari, ya tabbatar da cewa matatun Fatakwal da Kaduna su ma suna kan aiki, kuma ana sa ran za su fara samar da mai nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana cewa manyan matatun kasar guda hudu da suka haɗa da na Warri, tsohon Fatakwal, sabuwar Fatakwal, da Kaduna, suna kan hanyar farfadowa bayan matsalolin da suka faru da masu fasa bututun mai a baya.
A baya, Nijeriya ta fuskanci wahalar tace ɗanyen mai sakamakon lalacewar bututun mai da ke kai ɗanyen mai zuwa matatun ƙasar.
Sai dai da farfaɗowar matatun, ana sa ran farashin litar mai zai yi sauƙi tare da wadatar mai a kasuwa.