Wani sabon bincike da Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), ya gudanar ya gano yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja da jihar Nasarawa.
Bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewa a Nasarawa da babban birnin tarayya, mazauna garin na cikin takaici saboda karin farashin kayan abinci.
- Buhari Ya Roki ASUU Kan Sake Duba Matsayarsu Ta Yajin Aiki
- Abinda Yasa Na Zabi Musulmi Mataimakina – Tinubu
Wani dan kasuwa a kasuwar Kubwa, Dini Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun wake kan Naira 27,000 amma yanzu a na sayar da shi kan Naira 49,000.
Suleiman, ya ce a baya ana sayar da buhun shinkafa ‘yar gida tsakanin N15,000 zuwa N20,000, inda ya ce a yanzu ana sayar da shi kan Naira 29,000, yayin da buhun shinkafar kasar waje da ake sayar da ita kan Naira 25,000 yanzu ta koma N34,000.
Buhun gari mai launin rawaya, wanda ake sayarwa a kan N8,000, a halin yanzu ana sayar da shi kan N22,000 yayin da farin gari da ake sayarwa a kan N6,000 a halin yanzu ana sayar da shi a kan N17,000.
Suleiman ya kara da cewa buhun masara a baya ana sayar da shi kan N6,000 yanzu ya koma N20,000.
Ya alakanta hauhawar farashin kayan abincin da tsadar sufuri, wanda ya ce hakan ya shafi karfin saye, wanda hakan ya sa farashin kayan abincin ke ci gaba da tashi.
Tsadar kayayyakin ba iya birnin tarayya da jihar Nasarawa ta tsaya ba, lamarin ya shafi ko ina a fadin Nijeriya.