Babban jami’i a sashen lura da ayyukan hadin gwiwar rundunonin sojoji, karkashin babban hukumar gudanarwar rundunar sojin kasar ta Sin Wu Zeke, ya ce babban faretin sojoji da za a yi ranar 3 ga watan Satumba dake tafe a filin taruwar jama’a na Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing, na da nufin nunawa duniya aniyar kasar Sin ta goyon bayan zaman lafiya, da kare gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa.
Wu Zeke ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Laraba dangane da shirye-shiryen gudanar da faretin, wanda aka tsara domin bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar dakarun Japan da yakin kin tafarkin murdiya.
Jami’in ya kara da cewa, faretin zai nuna yadda karkashin jagorancin JKS, kasar Sin da rundunar sojojinta suka samu karfin ci gaba, da dorewar ruhin yakin kare kai daga mamaya.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da kasashe, da al’ummun sassan duniya daban daban masu kaunar zaman lafiya, wajen bunkasa, da yayata ainihin abubuwan da suka faru a tarihi yayin yakin duniya na biyu, da burin kasar na kare odar kasa da kasa bayan yakin, da kare kimar gaskiya da adalci, da dagewa wajen nuna adawa da dukkanin nau’o’in danniya, da siyasar nuna karfi, da ma hada hannu wajen mara baya ga gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp