Bisa alkaluman baya bayan nan da ma’aikatar harkokin noma da raya kauyuka ta kasar Sin ta fitar, tun daga farkon shekarar bana, masana’antun Sin a fannoni daban daban, kamar na sarrafa amfanin gona, da yawon shakatawa na kauyuka na kara samun ci gaba sosai.
Tun daga shekarar bana, ma’aikatar noma da raya kauyuka ta Sin ta gudanar da aikin bunkasa masana’antun sarrafa amfanin gona, kana daga watan Janairu zuwa watan Yuni, manyan masana’antun sarrafa amfanin gona sun samu kudin shiga da ya kai yuan tiriliyan 8.7, adadin da ya karu da kaso 1.1 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara.
- Sin Ta Ki Amincewa Da Duk Wanda Ya Yi Amfani Da Gasar Olympics Wajen Yada Yunkurin ‘Yan Aware Na Yankin Taiwan
- CCCEU: Harajin EU Kan Motocin Lantarki Zai Kawo Cikas Ga Burin Daidaita Sauyin Yanayi
Ban da haka, sashen yawon shakatawa na karkara na Sin, shi ma ya samu ci gaba sannu a hankali, inda ya samu sakamako mai kyau daga watan Janairu zuwa watan Maris, ya kuma ci gaba da kyautatuwa daga watan Afrilu zuwa watan Yuli.
Ya zuwa yanzu, gaba daya an riga an gina muhimman gundumomin aikin noma 180, da kuma kyawawawan kauyuka guda 1,953 a kasar Sin.
Buku da kari, ma’aikatar aikin noma da raya kauyuka ta kasar, ta aiwatar da matakan bunkasa masana’antun aikin noma, don inganta saurin bunkasar masana’antun halayyarar musamman na kauyuka. (Safiyah Ma)