Kungiyar ‘yan kasuwa ta kasar Sin a Tarayyar Turai wato CCCEU ta sake nanata a jiya Juma’a cewa, sanya haraji mai yawa kan shigo da motocin lantarki na batir (BEVs) daga kasar Sin da EU za ta yi, zai kawo cikas matuka ga manufofinta na daidaita sauyin yanayi, da kwarewar yin takara a fannin masana’antu, da hadin gwiwar Sin da EU a fannin kera motoci.
A cikin wata sanarwar da ta fitar, kungiyar CCCEU ta ce, fara amfani da motocin lantarki na da matukar muhimmanci ga EU wajen cimma burinta na daidaita sauyin yanayi, kuma sanya haraji mai yawa a kan BEVs na kasar Sin zai kara tsadar farashinsu ne kawai, da rage bukatar masu amfani da su, kuma zai kawo jinkiri ga kokarin EU na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da daidaiton yanayi.
Tarihi na masana’antar kera motoci ta duniya ya nuna akai-akai cewa, kariya na iya kawo tsadar samar da hajoji tare da sanya kamfanoni su daina yin gasa a karkashin inuwar haraji, a cewar kungiyar. (Yahaya)