Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce, a shirye ta ke ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana a ranar Asabar.
Sai dai hukumar ta ce, ta shiga damuwa matuka kan rahoton da kwamishinan zabe na jihar ya bayar na barazana ga ofishin INEC da ke karamar hukumar Okpoba-Okha a ranar Asabar, wanda ya haifar da turmutsitsin da ya jikkata daya daga cikin jami’anta.
- Zaben Edo: Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna A LP, Ya Sha Kaye A Mazaɓarsa
- Jarumai A Masana’antar Kannywood Sun Jajanta Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri
INEC ta kuma nuna damuwarta kan yadda wasu ‘yan siyasa da magoya bayansu suka hallara tare da gudanar da zanga-zanga a babban ofishinta da ke birnin Benin, babban birnin jihar, gabanin fara tattara sakamakon zaben.
Kwamishinan INEC na kasa, kuma mamba a kwamitin Watsa Labarai da wayar da kan masu zabe, Mohammed Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Lahadi.
Ya ce, babu wanda ya isa ya kawo cikas ga tsarin tattara sakamakon zaben a kowane mataki kuma ba za a bari wani ya ci gajiyar shirin taka doka da oda ba.