A ci gaba da daukar matakan shawo kan hauhawar farashin abinci da tsadar rayuwa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a ranar Talata ta ce ta cafke wasu manyan motoci 141 da ke yunkurin safarar hatsi da sauran kayayyakin abinci zuwa Kasashen Jamhuriyar Nijar, Chadi, Kamaru, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Kwanturolan Hukumar Hana Fasa Kwauri na Nijeriya, Bashir Adeniyi, ya ce a cikin makonni biyu hukumar ta kama kimanin tireloli 120 da suka yi safarar kayan abinci daga Nijeriya, yayin da Hukumar EFCC ta hana manyan motocin abinci 21 barin kasar.
- Kabilanci Da Magudin Zabe Ke Kassara Samun Shugabanci Nagari – Jonathan
- An Rufe Taron Koli Na Kafofin Yada Labarai Dangane Da Kwaikwayon Hazikancin Dan Adam A Afrika
A yayin da Kwanturola Janar Na Hukumar ke bayyana matakan da ake dauka na tabbatar da wadatar abinci a majalisar wakilai da ke Abuja, direbobin manyan motocin da ke fuskantar hare-haren bata gari don kwashe kayan abinci, sun yi barazanar cewa za su shiga yajin aiki idaka ci gaba hana su aikinsu.
Motoci da ma’ajiyar kaya da dama mallakin masana’antu da sauran ma’aikatu masu zaman kansu sun fuskanci hare-hare daga wasu bata gari yayin da hauhawar farashin kayan abinci da kuma tsadar rayuwa ke kara kamari a kasar.
Ko a makon da ya gabata ma wasu matasa suka daka wa wasu manyan motocin dakon kayan abinci wawa da suka makale a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Suleja ta Jihar Neja.
Sannan an kai hari a wani rumbun ajiyar kaya na Sakatariyar Noma da Raya Karkara ta Gwamnatin Tarayya da ke unguwar Dei-Dei a Babban Birnin Tarayya inda suka yi awon gaba da shinkafa da hatsi da sauran kayayyakin agaji.
Kazalika wasu bata-gari sun sake kai farmaki wani rumbum ajiyar kaya da ke unguwar Idu Industrial Estate, Jabi, Abuja, amma sojojin da ke gadin ginin sun dakile shirin nasu.
Bugu da kari, wasu matasa sun kai hari kan motocin da ke jigilar kayayyakin gini da wata mota dauke da taliyar spaghetti a jihohin Ogun da Kaduna.
Cikin nuna damuwa da ci gaban da aikata abubuwan da ba su dace ba, kungiyoyi masu zaman kansu sun yi gargadin cewa hare-haren na iya haifar da rufe masana’antu a duk fadin kasar.
Da yake yi wa ’yan majalisar tarayya bayani kan aiwatar da umarnin da shugaban kasa ya bayar na dakile safarar abinci a lokacin ganawar tasu, Shugaban Hukumar Kwastam, Adeniyi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a karkatar da manyan motocin da aka kama zuwa kasuwannin yankin da suke wadanda an kama su ne domin kawo karshen hauhawar farashin hatsi da sauran kayan abinci.
Manyan motocin dakon abinci 120
“A cikin makonni biyu mun cafke kimanin tireloli 120 na kayan abinci da za su fita daga kasar. Wadannan su ne kayan abinci da shugaban kasa ya bukaci mu mayar wa kasuwannin cikin gida. Mun yi imanin hakan zai rage hauhawar farashin kayan abinci a wadannan wuraren,” in ji shi.
Ya ce an yanke shawarar dakatar da safarar kayan abinci ne domin a yaki yunwa da kuma dakatar da masu karfafa wa masu son arzuta kansu da dukiyar al’umma.
Ya kuma yi gargadi kan daukar matakan gaggawa don magance matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar, inda ya kara da cewa dole ne kasar ta dauki matakai na dogon lokaci domin shawo kan lamarin.
Adeniyi ya bayyana cewa hukumar kwastam na taka rawar gani wajen ganin an shawo kan matsalar samar da abinci, inda ya kara da cewa a halin yanzu galibin abubuwan da ake amfani da su na noma suna jawo rashin biyan haraji da karin haraji.
Kwanturolan ya lura cewa bukatar darasin da aka koya a lokacin da ake gwanjon kayan abinci da aka kama a Legas shi ya sa hukumar ta fara aiwatar da shirin a wajen Jihar Legas.
Kimanin mutum bakwai ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a shalkwatar hukumar NCS da ke unguwar Yaba a Jihar Legas a lokacin da ake gwanjon buhunan shinkafa da Hukumar NCS ta kwace a hannun masu fasa kwauri a watan jiya.
Lamarin ya tilastawa hukumomi dakatar da gudanar da aikin.
Da yake jawabi ga ’yan majalisar kan yadda za a yi gwanjon kayan ga jama’a, Adeniyi ya ce, Shugaba Tinubu ya umurci hukumar NCS ta yi gwanjon kayan ga marasa galihu a Nijeriya, yana mai cewa an fara aiwatar da shirin ne a Legas, amma daga baya aka hana.
Adeniyi ya ci gaba da cewa, kayayyakin abincin da aka kama za a sayar da su ne a kasuwannin cikin gida a fadin kasar nan bisa umarnin shugaban kasa.
Adeniyi ya ci gaba da cewa, abincin da aka kama za a sayar dasu ne a sauka cikin gida a fadin kasar nan bisa tsarin kasa.
Ya ce, “Shugaban kasa ya ba da umarnin mu sayar wa ‘yan Nijeriya mabukata kayan abinci da aka kama wadanda ake samarwa a cikin gida kai tsaye. Wannan yana daya daga cikin hanyoyin magance yunwa da karancin abinci da muke fuskanta, kuma mun fara wannan aiwatar da wannan aiki a Legas.