Ko makaho ya shafa, ya san yadda kimiyya da fasaha ke ci gaba taka gagarumar muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi a daukacin sassan rayuwar bil’adama ta yau da kullum a duk fadin duniya. Kasar Sin na ci gaba da amfani da fasahohinta na zamanantarwa wajen kirkire-kirkire da kawo sabbin salo.
Da yake kasar tana shirin karbar bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta shekarar 2025 daga ranar 7 zuwa 17 ga Agusta, yanzu haka ta kera wasu mutum-mutumi na ’yan sanda da suka fara sintiri a hukumance a birnin Chengdu dake lardin Sichuan na yankin kudu maso yammacin kasar.
- ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
- An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano
’Yan sandan mutum-mutumin sun tsunduma aiki tare da jami’ai abokan aikinsu a dandalin Tianfu, daya daga cikin wuraren da aka fi samun kai-komon mutane da kafa a kalla 100,000 a kullum. Da kansu suke sauya wurin aiki a tsakaninsu duk bayan awa biyu zuwa uku inda suke nadar murya da bidiyon abubuwan dake faruwa tare da aikawa nan take ga jami’an ’yan sandan dake kusa. A ranar 16 ga Yunin da ya gabata ne aka fara gwada ayyukan ’yan sandan na mutum-mutumi da nufin kara inganta amfani da su a birane.
An saya musu fasahar iya sadarwa, da yadda za su iya ba da taimakon aikin ’yan sanda ga masu yawon bude ido, da kula da zirga-zirgar ababen hawa, sannan da kansu suke kai kansu wurin caji don tabbatar da cewa aikinsu bai tsaya ba. Akwai abubuwan mamaki da yawa da wadannan ’yan sanda ke iya yi ciki har da gano mara lafiya a cikin masu yawon bude ido tare da kiran tawagar kawo daukin gaggawa.
Wannan fasaha za ta iya taimakon kasashenmu na Afirka wajen shawo kan matsalolin tsaro da dama duba da cewa har yanzu muna da karancin jami’an tsaro. Kididdigar da na gani daga shafin rumbun bayanai na Wikipedia na nuna cewa, a Nijeriya, mai yawan al’umma fiye da miliyan 230, duk dan sanda daya yana ba da tsaro ne ga kusan mutane 1000 ko kuma a ce duk ’yan sanda biyu suna kula ne da tsaron mutum 2,000. Kazalika, idan aka leka sauran kasashenmu na Afirka ma za a ga irin wannan gibin.
Idan za a yi amfani da wannan fasaha ta ’yan sandan mutum-mutumin inji ana iya rage yawan jami’ai da ake jibgewa a wuraren shafaffu da mai tare da kai su yankunan da ake fama da matsalar tsaro musamman na karkara.
Kar wani ya yi tunanin ko idan an dauki ’yan sanda daga birane zuwa karkara kamar an yi musu ba daidai ba, a’a, a ko ina aiki ya kama dole a je. Kuma da kudin kasa ake biyansu albashi ba kudin ’yan birni ba kawai. Su ma mazauna birane za su ci gajiyar hakan, don ’yan sandan mutum-mutumin za su yi aiki babu kakkautawa, tun da ba su bukatar barci, ko cin abinci, ko zaga bayi, da sauran wasu abubuwa na lalurorin dan’adam. Tabbas, amfani da su, zai kara yalwata jami’an ’yan sanda da ake bukata wurin gudanar da ayyukan tsaro ta yadda za a share wa al’umma hawaye ta fuskar matsalar tsaron da ake fama da ita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp