A shekarun baya, lokacin da na yi aiki a Najeriya, na taba kai ziyara jihar Lagos dake kudancin kasar, inda na shafe sa’o’i 5 a hanya tsakanin filin saukar jirgin sama zuwa tsibirin Victoria ta mota, duk da cewa tsawon tafiyar bai wuce kilomita 30 ba. A waccan lokaci, a ganina, Lagos birni ne matukar cunkoso.
Kwanan baya, wani aboki na dake Lagos ya bayyana min cewa, an fara amfani da jirgin kasa a Lagos, wanda kamfanin kasar Sin ya gina, kuma jirgi mai inganci yana taimaka masa rage lokacin da yake shafewa a kan hanya. Ya yi farin ciki sosai, inda ya ce, “A da ina shafe sa’o’i 3 a kan hanya, amma a yanzu ba na wuce mintoci 25, aikin da kamfanin Sin ke yi na da inganci matuka.”
Wannan layin dogo na jirgin kasa, shi ne irinsa na farko da kamfanin CCECC ya aiwatar a yammacin Afirka, wanda wani kamfanin Sin ya tsara, ya gina tare da aiwatarwa. Yana kuma da tsawon kilomita 13 da tasoshi 5, kuma shi ne layin farko da ya ratsa yammacin Lagos dake da yawan cunkoson jama’a.
An yi kiyasin cewa, wannan layin dogo zai rika yin jigirar fasinja dubu 175 a kowace rana, inda za a fara da zirga-zirgar sau 12 a kowace rana cikin makwanni 2, daga baya kuma a kara adadin.
Ba shakka, jirgin kasan ya rage lokacin da za a kwashe a kan hanya, kuma ya daga ingancin zaman rayuwar jama’a a wurin, kana ya mai da Lagos daya daga wasu biranen dake iya jigilar mutane mafiya yawa a Afirka, matakin da ya daga karfinsa na yin takara.
Fasahar kasar Sin na taimakawa Lagos, wajen warware matsalar toshewar hanya, da ma kyautata zaman rayuwar jama’a, da ciyar da bunkasuwar tattalin arziki gaba, wanda hakan ke faranta ran al’ummar Najeriya. (Mai zana da rubuta: MINA)