Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda ta samu wakilcin masana hada shayi da ‘yan wasan kwaikwayo na Yue Opera da masu wasan kayan Pipa.
Taron ya samu halartar mutane daga dukkan bangarorin rayuwa da suka hada da jami’an diplomasiyya da na gwamnati da malamai da daliban sakandare da ‘yan wasa da manema labarai da masoya al’adun shayi ta kasar Sin. An kuma gabatar da fasahar rubutun gargajiya ta Sin da zanen fenti da hotunan dake bayyana al’adu da wuraren bude ido na Zhejiang. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp