An kama wata mata ‘yar Nijeriya a tashar jirgin kasa a Kasar Indiya dauke da miyagun kwayoyi da aka kiyasta kudinsu ya haura Naira biliyan 6 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan hudu, kamar yadda jaridar PUNCH Metro ta gano.
An kama Etumudon a tashar jirgin kasa ta Panbel, Maharashtra, tare da jaririnta mai suna Miracle.
- Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
- ADC Ga Tinubu: Ina Wutar Lantarki Ta Awa 24 Da Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Alkawari?
A cewar wani rahoto da wata kafar yada labaran intanet ta Indiya, Deccan Herald, ta bayar a ranar Asabar, an gudanar da aikin hadin gwiwa ne da Rundunar Kariya ta Railway, na Central Railway, Panbel; Ofishin Kula da Narcotics, Bengaluru; da Reshen Leken asirin Laifuka, Kurla, Mumbai.
An ruwaito wanda ake zargin yana cikin jirgin kasa mai lamba 12618 Hazrat Nizamuddin–Ernakulam Mangala Edpress, kuma an kama shi ne sakamakon bayanan sirri da NCB Bengaluru ta samu.
“Aiki da takamaiman bayanan sirri, an kaddamar da aikin haɗin gwiwa kuma an gudanar da bincike a kan isowar jirgin a Platform No. 7, Panbel Railway Station,” in ji jami’an CR.
A yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike a yankin, rahotanni sun ce jami’an sun gano wata mata ‘yar Nijeriya a Coach A-2, Seat No. 27, tare da wani yaro da wata jakar balaguro kala-kala.
Rahoton ya bayyana cewa bayan an yi mata tambayoyi, ta bayyana sunanta Doris daga Nijeriya kuma ta ce yaron da ke tare da ita, wanda ta bayyana sunansa Miracle, nata ne.
RPF ta lura cewa “da aka yi mata tambayoyi a gaban shaidu masu zaman kansu, matar ta amsa cewa tana dauke da kayan maye.”
Daga baya an kai ta zuwa gidan RPF a Panbel domin cikakken bincike.
Rahoton ya lura cewa a cikin jakar balaguron, jami’an sun gano bakaken fakiti guda biyu da aka lullube da kayan roba da aka yi wa lakabi da “BINTAGE.”
A cewar ‘yansanda, na’urorin gwajin muggan kwayoyi daga baya sun tabbatar da cewa abin da ke ciki hodar iblis ce mai nauyin kilogiram 2.002.
Binciken da aka yi a baya ya gano wata jakar Mickey Mouse mai ja-da-shudi ta yara da ta boye a cikin babbar jakar.
‘Yansandan sun bayyana cewa karamar jakar na dauke da fakitin takardu guda biyu – daya mai lakabin “Kellogg’s Corn Flakes” da sauran “Bongchi Perfect Roll.”
An samu rahoton cewa wadannan suna dauke da fararen sinadarai na crystalline, daga baya aka gano su da methamphetamine, mai nauyin kilogiram 1.488.
Hukumomin CR sun tabbatar da cewa “magungunan da aka kama, darajarsu ta kai kusan Rs 36 crore”
Etumudon ta zama mace ta biyu ‘yar Nijeriya da aka kama a Indiya cikin kasa da watanni biyu bisa laifin safarar muggan kwayoyi.
Ta bi sahun wasu ‘yan Nijeriya da dama da a halin yanzu ke fuskantar shari’a a kasar kan irin wadannan laifuka.
“Aikin da aka gudanar cikin bayanan sirri, an kaddamar da shi ne da hadin gwiwa kuma an gudanar da bincike a kan isowar jirgin a Platform No. 7, Panbel Railway Station,” in ji jami’an CR.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp