Wani fashewar bam ya auku a makarantar Islamiyya da ke unguwar Kuchibiyu, yankin ƙaramar hukumar Bwari a Abuja, inda ya yi sanadin mutuwar ɗalibi ɗaya da jikkata wasu huɗu yau Litinin.
Wata majiya ta tsaro ta tabbatar da cewa fashewar ta faru ne da rana, inda tawagar gaggawa da jami’an tsaro, ciki har da tawagar cire bam na ‘yansanda, suka isa wurin. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.
- Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Litar Mai Zuwa Naira 965 A Abuja
- Dalilin Da Ya Sa Legas, Abuja, Kaduna Suka Samu Masu Zuba Hannun Jari A Zango Na Uku
A halin yanzu, ba a samu cikakken bayani kan dalilin fashewar ba, kuma ba a sami wata sanarwa daga ‘yansanda ko mahukuntan makarantar ba a lokacin tattara rahoton nan.
Cikakkun bayanai na tafe…