Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Tarayya (FEMA) ta ce fashewar wata tankar gas ce ta janyo gobarar da ta haddasa mutuwar mutane biyu da kuma raunata wasu karin biyu a ofishin jakadancinta Canada da ke Abuja.
Gwamnatin kasar Canada ta ce ta gamsu ba harin ta’addanci ba ne ya yi sadiyyar fashewar da ya faru a ofishinta ba.
- Abarbar Benin Ta Shaida Yadda Kasar Sin Ke Kara Bude Kofarta
- Gargaɗin Amurka Kan Nijeriya Na Tada Hankulan Masu Zuba Jari A Kasar – Minista
Cikin wata sanarwa da ofishin Jakadancin ya fitar a Abuja, ya ce kawo yanzu bisa bayanan da ake da shi a hannu, ana iya cewa gobara ce ta jawo fashewar ba wani aikin ta’addanci ba.
”Mun tabbatar da cewa dukkannin ma’aikatan ofishin jakadancinmu da ke Abuja suna nan lafiya, ba wanda ya samu rauni, kuma muna aiki da hukumomin Nijeriya don gano ainihin abin da ya faru. Za a gudanar da bincike amma dai a halin yanzu, muna ganin hatsari ne kawai ya faru” a cewar sanarwar.
Biyo bayan wannan fashewa dai, ofishin jakadancin na Canada ya dakatar da ayyukansa har zuwa wani lokaci.
Kakakin hukumar bada agajin gaggawar, Nkechi Isa cikin sanarwar da ta sanyawa hanu, ta ce fashewar ta kuma kone wani sashe na ofishin jakadancin.
“Da misalin karfe 10:45 na safiyar Litinin ne lokacin da ake gyara Janarta samfurin MIKANO. “A daidai lokacin da janeraten ke aiki, wata motar tanki mai dauke da gas 2000 ta fashe abin da kenan da ya haddasa gobarar” a cewar sanarwar.
Tuni dai shugaba Bola Tinubu ya mika sakon jaje ga gwamnatin kasar Canada, da kuma ta’aziyya ga ‘yan uwa da iyalan wadanda su ka rasa rayukansu, inda ya bayyana hakan a matsayin babban abin bakin ciki.