Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 12 a wani mummunan hatsarin da ya auku a Jihar Ebonyi.
An bayyana cewa 10 daga cikin wadanda abin ya shafa mata ne yayin da biyu kuma maza ne.
- Xi Jinping Ya Kai Rangadi A Lardin Guangdong
- El-Rufai Ya Jinjina Wa Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Danwasa A Kaduna
An tattaro cewa hatsarin ya auku ne a unguwar Ezzillo da ke kan hanyar Abakaliki zuwa Enugu.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa wadanda lamarin ya shafa sun yi hayar motar EBSU mai kujeru 14 daga Abakaliki zuwa Jihar Enugu domin halartar jana’iza.
Wani ganau da ya zanta da manema labarai a Abakaliki, ya ce motar bas din EBSU ta yi karo da wata babbar mota da ta ke kan hanyar dawowa daga Jihar Enugu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan sashen FRSC na Ebonyi, Uche Chukwurah ya ce hatsarin ya hada da wata mota kirar bas da wata babbar mota.
Chukwurah ya tabbatar da cewa mutanen da ke cikin motar bas din su 14, mata guda 12 da maza biyu.
Ya ce mutanen biyu sun samu munanan raunuka sakamakon hatsarin da ya auku a safiyar ranar Talata.
“Hatsarin ya rutsa da motar bas da wata babbar mota. Fasinjoji 14 ne lamarin ya rutsa da su. 12 daga cikinsu sun mutu; 10 mata, sai mutum biyu maza. Mutanen biyu da suka jikkata suna asibiti,” in ji kwamandan sashen.