Sabon mai tsaron ragar da Manchester United ta saya ya bayyana cewa ya yi
farin cikin komawa kungiyar a wannan lokacin kuma yana fatan lashe kofin zakarun Turai a kungiyar.
Manchester United ta amince da tayin fam miliyan 47.2 domin sayen Andre Onana mai tsaron ragar, Inter Milan kuma kungiyar ta biya fam miliyan 43.8 wajen sayen mai tsaron ragar tawagar Kamaru da karin fam miliyan 3.4 na tsarabe-tsarabe.
Manchester United na fatan dan kwallon mai shekara 27 zai je Amurka don buga mata wasannin atisaye da za ta buga dominn tunkarar kaka mai zuwa, amma sai an nemar masa takardar izinin zuwa kasar. Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya bukaci a sayo masa dan wasan a karshen kakar da ta wuce, wanda ya horar da shi a kungiyar kwallon kafa ta Ajad shekaru uku da suka gabata.
Ten Hag yana ganin Onana zai taimaka wa Manchester United a wasannin kakar wasa ta 2023 zuwa 2024, hakan ya sa Dabid de Gea ya zabi barin United, bayan da aka bukaci ya tsawaita zamansa.
Onana ya yi kaka bakwai da rabi a Ajad, daga nan ya koma Inter a Yulin shekara ta 2022 kuma ya yi wasa takwas kwallo bai shiga ragarsa ba a karawa 24 a Serie A, yayin da Inter ta kammala a mataki na uku a teburin babbar gasar Italiya.
Haka kuma ya yi wasanni 13 a Champions League da kwallo bai shiga ragarsa ba a fafatawa takwas, inda Inter ta yi ta biyu a gasar, bayan da Manchester City ta lashe kofin.
Onana shi ne na biyu da Manchester United ta dauka a bana kenan, bayan sayen Mason Mount daga Chelsea kan fam miliyan 55 kuma yanzu kungiyar tana zawarcin dan wasan Atlanta, Rasmus Hojlund, dan asalin kasar Denmark.