Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) na farautar wani dan Nijeriya bayan da ya damfari Gwamnatin New York kudaden da yawansu ya zarta Dala miliyan 30 kwatankwacin Naira biliyan 15.
Wata sanarwa da ofishin babban lauyan Amurka ya fitar, ta ce ana tuhumar Chodize Collins Obasi, mai shekaru 29 da aikata laifuka da dama da suka hada da damfara ta hanyar aika sakonni ta Intanet.
- Sin Ta Tallafa Wa Falasdin Da Kudi Dala Miliyan 1 Don Inganta Ilimin Yara
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Za Su Samar Da Kamfanin Zirga-zirgan Jirgin Sama
A farkon barkewar cutar Korona, Obasi ya sayarwa da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na Amurka na’ urar numfashi ta bogi, kafin daga bisani ya saci bayanan wani Ba’amurke, inda ya yi ta karbar kudaden rage radadin cutar Korona da sunansa.
Hukumomin Amurka sun ce Obasi ba shi kadai yake aikin damfafar ba domin kuwa yana da wasu mataimaka a kasar Kanada, amma daga Nijeriya yake gudanar da nasa ayyukan na damfara.
Muddin dai FBI ta yi nasarar cafke Obasi, to lallai zai fusakanci hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 621 a gidan yari, da kuma cin tarar Dala miliyan miliyan 5 da dubu 750.
Kazalika, hukumomin Amurka za su tilasta masa dawo da kudadaen da ya sata da suka zarta Dala miliyan 31, kamar yadda jaridar RFI ta wallafa.