Kasar Sin ta tallafa wa Falasdin da kudi Dala miliyan daya domin inganta ilimi da rayuwar yara kananan.
Sin din ta aika da wannan gudunmawa ne ta hannun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, domin tallafawa ilimin da kuma rayuwar kananan yara ga al’ummar Yammacin Kogin Jodan.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Da Dama
- Ganduje Ya Amince Da Biyan Miliyan 304 Na Alawus Ga Malaman Jami’ar Gwamnatin Kano
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, Kasar Sin ta bayar da kudin ne don samar wa daliban ‘yan gudun hijirar Falasdinu damar samun ilimi mai inganci, daidaito da kuma hada kai ta hanyar shirin ba da ilimi na UNRWA.
Sanarwar ta ci gaba cewa taimakon karamcin daga kasar Sin din UNRWA, za a yi amfani da shi ne wajen ilmantar da dalibai kimani 9,200, a makarantu 19 da ke gabar Yammacin Kogin Jodan na tsawon watanni biyu a wannan shekarar.
Haka kuma Hukumar ta UNRWA, ta nuna matukar godiya ga gwamnatin Kasar Sin bisa goyon baya da sadaukar da kai da take ci gaba da bai wa ‘ yan gudun hijirar Falasdinu.
Karin Aamer jami’ in UNRWA ya ce, “Muna matukar godiya da kyakkyawar dangantakarmu da Kasar Sin, wadda ke ci gaba da bunkasa da kuma fadada.