Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta sanar da amincewar kuɗin kujerar aikin Hajjin shekarar 2026 a kan Naira miliyan 8,244,813.67 ga kowane mahajjaci tare da bayar da wa’adin ƙarshen watan Disamba na 2025 don kammala biyan dukkan kudaden.
A wata sanarwa da Daraktan Hukumar, Malam Kadiri Edah ya fitar a ranar Litinin, ya buƙaci mahajjatan da ke son zuwa aikin Hajji su tabbatar da biyan cikakken kudin kafin cikar wa’adin don samun kujerar zuwa kasar mai tsarki.
Edah ya yi gargadin cewa, “Dukkanin kuɗaɗen da za a biya hukumar dole ne a biya su ta hanyar asusun banki, ba a amince da karɓar tsabar kuɗi ba.”
Ya bayyana cewa, bin wannan ƙa’idojin yana da matukar muhimmanci domin bai wa hukumar damar tattara sahihin jerin sunayen maniyyata da kuma tura dukkan kuɗaɗen zuwa ga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a kan lokaci.
Ya shawarci maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu da su miƙa takardunsu na tafiya cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp