Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA, a cigaba da aikin rusau a karamar hukumar Kuje, ta rusa wani karamin Jerin-gidaje da gidaje da wuraren ibada da otal-otal da gidan cin abinci, da sauran wasu haramtattun gine-gine da aka gina a kan titin jirgin kasa dake yankin.
Jami’an FCTA sun futo cikin tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa ne dauke da bindigu sun mamaye yankin a ranar Litinin din da ta gabata don fara aikin rusa haramtattun gine-ginen, FCTA ta fara rushe gine-ginen da ke kan manyan tituna ne a cikin garin Kuje tare da rusa wasu manyan gine-gine a kan titin jirgin kasa, a jiya Talata.
Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa, da aiwatar da aiki ga ministan babban birnin tarayya, Kwamared Ikharo Attah, ya ce za a ci gaba da rusa haramtattun gine-ginen dake kan layin dogo na Kuje na tsawon kwanaki har sai an kwato duk filayen hukumar jirgin kasan da jama’a suka mamaye.
Ya kara da cewa ministan babban birnin tarayya, ba zai yi kasa a gwiwa ba har sai an kwato filayen hanyoyin jirgin kasan. Ya ce, “Tsaftar layin dogo na Kuje na daya daga cikin manyan ayyukan da FCTA ta sa gaba duk da cewa ruguje gine-ginen Jama’a na da matukar ban tausayi.
“Jami’an mu, zuciyarsu ta kadu sosai don tausayi wajen yin wannan rusau din, wasu ma sun kusa zubar da hawaye, ganin cewa wadanda lamarin ya rutsa da su, basu Kwashe kayayyakinsu ba daga cikin haramtattun gine-ginen.”