Hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) Abuja, za ta rushe dukkanin gine-ginen da mutane suka yi a filin da aka ware na layin dogo (Jirgin kasa) da ke yankin Kuje ba tare da biyansu ko kwabo da sunan diyya ba.
FCTA ta sanar da hakan ne a karshen mako yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki tare da sarakunan gargajiyan yankin, inda hukumar ta nuna rashin jin dadinta bisa yadda mutane suka mamaye wuraren da aka ware na titin Jirgin kasan a yankin ba bisa ka’ida ba.
Babban mai taimakawa a bangaren bin diddigi da bibiya ga ministan babban birnin tarayya (FCT), Kwamared Ikharo Attah, ya Bayyana rashin jin dadin sa kan yadda Jama’a ke gini ba bisa ka’ida ba.
Ya sha alwashin rushe gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba, Inda yace, sisi ba za su biya ba a matsayin kudin diyya.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su gargadi wadanda suka shiga filayen da su tattara komatsansu su fice kafin lokacin da za a zo bukatar wuraren.