Gwamnatin jihar Neja ta yunkuro domin tabbatar da an ceto mata da ‘ya’yan tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC, Janar Idris Garba daga hannun masu garkuwa da mutane wadanda harin Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya shafa.
An sace matar tsohon gwamnan Maryam Bobbo, da ‘ya’yansa maza Abubakar da Ibrahim Idris Garba da kuma ‘ya’yansa uku Fatima, Imran da Zainab duk an yi garkuwa da su.
- Tarayyar Turai Za Ta Yi Nazari Kan Lafta Wa Rasha Karin Takunkumai
- An Dakatar Da Sarkin Da Ya Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A Zamfara
Sakataren Gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ne ya jagoranci tawagar gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello zuwa gidan tsohon gwamnan Kano, Wazirin Lapai kuma shugaban Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida a karshen mako.
Da ya ke misalta lamarin a matsayin abun tir da kaico na yin garkuwa da iyalansa har mutum shida, ya ce, harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya sake farkar da gwamantin Neja kan yaki da ‘yan ta’adda.
Ya roki iyalan Wazirin Lapai da sauran wadanda aka yi garkuwa da ahalinsu da su ji kwarin guiwa daga bangaren gwamnati na cewa ita gwamnatin za ta yi dukkanin mai yiyuwa wajen ganin iyalansu sun kubuta daga hannun ‘yan ta’addan.
Ya fada wa shugaban IBBU wakilan gwamnatin Neja, sun ziyarci gidansa ne domin tabbatar masa da cewa gwamantin jihar a kan kafafunta take wajen yaki da ‘yan ta’adda da tabbatar da cafke su a kowane lokaci.
Matane ya ce, “Shi (gwamna) ya umarci dukkanin hukumomin tsaro da su gaggauta daukan matakan ceto wadanda aka yi garkuwa da su, kuma da izinin Allah za su kubuta”.
“Mu gwamnati ne da muka san nauyin da ke kanmu kuma muna tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’ummar mu a kowani lokaci.”
Ya gargadi wadanda ke da hannu a aikace-aikacen ta’addanci da su fa sani gwamnati ba za ta taba barinsu suna cin karensu babu babbaka ba, don haka abun da ya fi musu kawai su gaggauta sauya matsayarsu su zama mutane ne kwarai.
Dukkanin wadanda suka yi magana a yayin ziyarar sun ce garkuwan da aka yi da iyalansu ya hanasu barci da sakewana kowani lokaci, sun roki gwamnati da ta yi duk mai yiyuwa wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su.