Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana jiya Jumma’a cewa, jarin ketare na kai tsaye da aka yi amfani da shi a babban yankin kasar Sin a watan Janairu, ya kai kudin Sin yuan biliyan 112.71, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 15.86, wanda ya ragu da kashi 11.7 bisa 100 kan na makamancin lokaci na shekarar bara, kuma ya karu da kashi 20.4 bisa 100 bisa ga watan Disamban shekarar bara.
A cewar ma’aikatar, a watan da ya gabata, an kafa sabbin kamfanonin waje 4,588 a fadin kasar, wanda ya karu da kashi 74.4 bisa 100 kan na shekarar bara. Wannan ya nuna cewa, masu jarin waje na da sha’awar zuwa kasar Sin, kuma har yanzu kamfanonin kasa da kasa suna da kyakkyawan fata game da damar samun ci gaba a kasuwannin kasar Sin.
- An Kama Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Mutane A Jihar Nasarawa
- Mata Na Da Jan Aikin Sanin Muhimmancin Kansu Ta Kowane Fanni – Farida Abubakar
Jarin ketare na kai tsaye (FDI) da aka zuba a cikin manyan masana’antu na fasaha, ya karu da kashi 40.6 bisa 100 kan na shekarar bara a watan Janairu.
Ma’aikatar ta ce, FDI daga kasar Faransa ya karu da ninki 25, kana daga kasar Sweden ya ninka sau 11, sannan daga kasashen Jamus, da Australia da Singapore kuma ya karu da kashi 211.8 bisa 100, kashi 186.1 da kashi 77.1 bisa 100, bi da bi.(Ibrahim)