Hukumar da ke kula da lafiyar hanyoyi gami da gyarasu (FERMA), a ranar Litinin, ta ce, tana bukatar naira biliyan dari (N100b) daga wajen gwamnatin tarayya domin gaggautawa da hanzarta gyara hanyoyin da suka lalace a fadin kasar nan sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu.
Daraktan gudanarwa na hukumar ta FERMA, Injiniya Nurudeen Abdulrahman Rafindadi, shi ne ya shaida hakan a harabar Majalisar Dokoki ta kasa sa’ilin kare kasafin 2023 a gaban mambobin Majalisar Dattawa kan FERMA.
Rafindadi, wanda ya shigar da bukatar lokacin da ke amsa tambayar Shugaban kwamitin Majalisar, Sanata Gershom Bassey (mamban PDP da ke wakiltar mazabar Kurus Ribas ta kudu), kan matakan da hukumar za ta dauka wajen gyara hanyoyin da ambaliyar ruwa ya lalata.
Ya ce, bibiya da hukumar ta yi, ta gano cewa naira biliyan dari din (N100b) ana bukatarsa ne cikin gaggawa don gyara hanyoyin da lamarin ya shafa a sassa daban-daban na kasar nan.
“FERMA tana da muhimmiyar rawar takawa wajen daidaita lamura a yankunan da aka samu ambaliya a bangaren samar da hanyoyin kai agajin gaggawan ko kayan tallafin rage radadi.
“Idan ba an sake gyara hanyoyin da suka lalace ba a sassan da aka samu ambaliyar nan, babu wani kayan rage radadi ko tallafin gaggawa da za a iya kai wa mutanen da lamarin ya day-daya.
“An rigaya an samu barna sosai a hanyoyi daban-daban na jihohin kasar nan, kuma akwai bukatar naira biliyan dari domin sake gyarawa,” a cewar Rafindadi.
Mambobin kwamitin Majalisar, sun tabbatar wa shugaban na FERMA cewa Majalisar za ta shiga cikin lamarin domin ganin an Samar wa hukumar wannan biliyan 100 domin gyara hanyoyin da suka lalace a fadin Nijeriya.