A daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan rikicin kasar Syria, shugabannin kasashen duniya sun nuna damuwarsu sakamakon faduwar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria da ya dade yana mulki, wanda rahotanni suka ce ya fice daga kasarsa bayan da aka kwace babban birnin kasar, Damascus.
Mayakan ‘yan adawar sun bai wa duniya mamaki ganin yadda sojojin Syria suka kasa yin galaba a kan dakarun ‘yan tawaye wadanda da yawansu masu da’awar Musulunci ne da ake zargin kasashen da ba a san ko su wanene ba ne ke marawa baya, lamarin da ke zama wani muhimmin sauyi na tarihi ga kasar da ke fama da rikici.
- Sin: Daga 2018 An Gurfanar Da Mutane 114,000 Kan Laifuka Masu Nasaba Da Amfani Da Mukami Ba Bisa Ka’ida Ba
- UNESCO Ta Sanya Karin Al’adun Gargajiya 3 Cikin Jerinta Na Al’adun Gargajiya Da Ba Na Kayayyaki Ba
Bayan kwace Damascus, ‘yan tawayen sun bayyana cewa an ‘yantar da kasar.
Sun sanar da cewa, shugaba Assad ya fice daga kasar ne a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwa a Damascus da ma wasu sassan kasar ciki har da kan iyakar kasar da Lebanon da ke makwabtaka da kasar, inda da dama daga cikin ‘yan Syria da suka rasa matsugunansu ke son komawa gida.
Assad ya sha gwagwarmayar ci gaba da mulki a cikin shekaru 13 na yakin da ya yi sanadin kashe dubban ‘yan Syria yayin da wasu da dama suka rasa matsugunansu.