• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ficewar Malam Shekarau Daga NNPP: Me Ya Sa Hankalin ‘Yan Kwankwasiyya Ya Tashi?

Shekarau Ya Raba Gari Da Kwankwaso A Kano

by Buhari Abba Rano
3 years ago
Shekarau

Tun bayan da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso, inda koma jam’iyyar PDP, ‘yan Kwankwasiyya a ciki da wajen Jihar Kano suka shiga bayyana takaicinsu tare da zafafa adawa a kan lamirin tsohon gwamnan.

Tun da farko Malam Shekarau, ya dauki matakin komawa jam’iyyar PDP ne sakamakon abin da ya kira “rashin adalci” da Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP.

  • ‘Yan Ta’adda Sun Raba Mutum Dubu 190 Da Muhallansu Cikin Shekaru 8 A Zamfara -Rahoto
  • Yajin Aikin ASUU: Sakacin Ministan Ilimi Ne —Atiku

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, Sanata Shekarau da al’ummarsa su ka koma jam’iyyar NNPP, sakamakon wani rikicin siyasa tsakaninsa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A lokacin da Shekaru ya koma jam’iyyar NNPP, mabiya darikar Kwankwasiyya da jagoransu sun yi ta yabon Malamin Sanatan tare da ikirarin cewa sun yi babban kamun da zai kai su ga nasarar lashe zaben Kano a 2023.

Amma wani abin mamaki irin na ‘yan Kwankwasiyyar shi ne, daga lokacin da aka fara rade-radin Malamin Sanatan zai koma jam’iyyar PDP, ai kuwa babu bata lokaci su ka durfafi yada jita-jita a kan Shekarau din da majalisar ta Shura babu kakkautawa musamman a shafukan sada zumunta na Intanet.

LABARAI MASU NASABA

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

‘Yan Kwankwasiyya sun fara da yada jita-jita a kan wai Sanata Shekarau din ya shiga jam’iyyar a makare dan haka babu damar a bai wa mutanesa takara a NNPP, daga nan kuma su ka koma jita-jitar cewa hayar mutane aka yi daga makotan jihohi domin tarbar dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Ana tafe dai kafin Shekarau din ya bayyana aniyarsa, ‘yan Kwankwasiyya suka ci gaba da yada labarai marasa tushe balle makama a kan cewa Atiku Abubakar ya bai wa tsohon gwamnan biliyoyin kudade tare da wani katafareren gida a birnin tarayya, Abuja, a matsayin tukuicin ficewa daga NNPP.

Kuma abin da zai bayar da mamaki shi ne yadda su ke cewa Shekarau din shi kadai ya fice kuma taronsu da Atiku Abubakar babu wanda ya halarta, sai dai wai an biya matuka baburan A-Daidaita-Sahu a birnin Kano Naira dubu uku da dari biyar (3,500), a kan cewa su je wajen taron Wazirin na Adamawa.

Abin mamakin shi ne duk da ikirarin na ‘yan Kwankwasiyya, amma tabbas ficewar Malam Ibrahim Shekarau ta tsaya musu a rai kuma taron jam’iyyar PDP ya tsone musu ido matuka, domin idan ka duba shafukansu na Facebook babu wani zance da su ke yi da ya wuce na ficewar Sanatan da kuma taron da dan takarar shugabancin Najeriya a PDP ya ke yi da magoya bayansa.

Masana harkokin siyasa na kallon ficewar Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wata dama ga nasarar Jam’iyyar APC da dan takarar ta na gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma rashin tabbacin nasarar Injiniya Abba Kabiru Yusuf da jami’yyar sa ta NNPP, wanda hakan ma wani karin dalili ne da ake ganin ya sa ‘yan Kwankwasiyyar sun fusata kan batun.

Hakazalika wani karin dalilin kuma shi ne yadda ana tsaka da gangamin taron su Sardaunan Kano din, sai wata kotun daukaka da ke zamanta a Abuja ta rushe shugabancin jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, wanda ake masa kallon yaran tsohon gwamna Kwankwaso ne da ya bari a jam’iyyar domin su bata ruwa tare da ƙara jefa jami’yyar cikin rudani.

Tabbas ficewar Malam Ibrahim Shekarau da taron Atiku Abubakar da tawagarsa bai kamata ya sa zuciyar ‘yan Kwankwasiyya ta kasa zama lafiya ba, domin suna da miliyoyin magoya baya da su ke da su a jam’iyyar NNPP da kuma mutum 45 da su ka yi wa Malamin gwamnan tutsu sun ishe su biyan bukatarsu a zaben 2023 a Jihar Kano da ma Najeriya, shi kuwa Shekarau da ‘yan Shura Umma ta gaida Aisha.

Haka kuma abin jira a gani shi ne ko Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, zai kai ga shiga filin zaben shugabancin Najeriya a kakar zaben 2023, ko shi ma zai karbi Awalaja kamar yadda magoya bayansa su ke zargin Shekarau ya yi? Lokaci ne zai tabbatar da haka!

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
Shekarau
Manyan Labarai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta
Siyasa

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
Next Post
Ba Zan Bari Kowa Ya Kawo Cikas A Zaben 2023 Ba – Buhari

Ba Zan Bari Kowa Ya Kawo Cikas A Zaben 2023 Ba - Buhari

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.