Tun bayan da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso, inda koma jam’iyyar PDP, ‘yan Kwankwasiyya a ciki da wajen Jihar Kano suka shiga bayyana takaicinsu tare da zafafa adawa a kan lamirin tsohon gwamnan.
Tun da farko Malam Shekarau, ya dauki matakin komawa jam’iyyar PDP ne sakamakon abin da ya kira “rashin adalci” da Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP.
- ‘Yan Ta’adda Sun Raba Mutum Dubu 190 Da Muhallansu Cikin Shekaru 8 A Zamfara -Rahoto
- Yajin Aikin ASUU: Sakacin Ministan Ilimi Ne —Atiku
A cikin watan Mayun da ya gabata ne, Sanata Shekarau da al’ummarsa su ka koma jam’iyyar NNPP, sakamakon wani rikicin siyasa tsakaninsa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A lokacin da Shekaru ya koma jam’iyyar NNPP, mabiya darikar Kwankwasiyya da jagoransu sun yi ta yabon Malamin Sanatan tare da ikirarin cewa sun yi babban kamun da zai kai su ga nasarar lashe zaben Kano a 2023.
Amma wani abin mamaki irin na ‘yan Kwankwasiyyar shi ne, daga lokacin da aka fara rade-radin Malamin Sanatan zai koma jam’iyyar PDP, ai kuwa babu bata lokaci su ka durfafi yada jita-jita a kan Shekarau din da majalisar ta Shura babu kakkautawa musamman a shafukan sada zumunta na Intanet.
‘Yan Kwankwasiyya sun fara da yada jita-jita a kan wai Sanata Shekarau din ya shiga jam’iyyar a makare dan haka babu damar a bai wa mutanesa takara a NNPP, daga nan kuma su ka koma jita-jitar cewa hayar mutane aka yi daga makotan jihohi domin tarbar dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Ana tafe dai kafin Shekarau din ya bayyana aniyarsa, ‘yan Kwankwasiyya suka ci gaba da yada labarai marasa tushe balle makama a kan cewa Atiku Abubakar ya bai wa tsohon gwamnan biliyoyin kudade tare da wani katafareren gida a birnin tarayya, Abuja, a matsayin tukuicin ficewa daga NNPP.
Kuma abin da zai bayar da mamaki shi ne yadda su ke cewa Shekarau din shi kadai ya fice kuma taronsu da Atiku Abubakar babu wanda ya halarta, sai dai wai an biya matuka baburan A-Daidaita-Sahu a birnin Kano Naira dubu uku da dari biyar (3,500), a kan cewa su je wajen taron Wazirin na Adamawa.
Abin mamakin shi ne duk da ikirarin na ‘yan Kwankwasiyya, amma tabbas ficewar Malam Ibrahim Shekarau ta tsaya musu a rai kuma taron jam’iyyar PDP ya tsone musu ido matuka, domin idan ka duba shafukansu na Facebook babu wani zance da su ke yi da ya wuce na ficewar Sanatan da kuma taron da dan takarar shugabancin Najeriya a PDP ya ke yi da magoya bayansa.
Masana harkokin siyasa na kallon ficewar Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wata dama ga nasarar Jam’iyyar APC da dan takarar ta na gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma rashin tabbacin nasarar Injiniya Abba Kabiru Yusuf da jami’yyar sa ta NNPP, wanda hakan ma wani karin dalili ne da ake ganin ya sa ‘yan Kwankwasiyyar sun fusata kan batun.
Hakazalika wani karin dalilin kuma shi ne yadda ana tsaka da gangamin taron su Sardaunan Kano din, sai wata kotun daukaka da ke zamanta a Abuja ta rushe shugabancin jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, wanda ake masa kallon yaran tsohon gwamna Kwankwaso ne da ya bari a jam’iyyar domin su bata ruwa tare da ƙara jefa jami’yyar cikin rudani.
Tabbas ficewar Malam Ibrahim Shekarau da taron Atiku Abubakar da tawagarsa bai kamata ya sa zuciyar ‘yan Kwankwasiyya ta kasa zama lafiya ba, domin suna da miliyoyin magoya baya da su ke da su a jam’iyyar NNPP da kuma mutum 45 da su ka yi wa Malamin gwamnan tutsu sun ishe su biyan bukatarsu a zaben 2023 a Jihar Kano da ma Najeriya, shi kuwa Shekarau da ‘yan Shura Umma ta gaida Aisha.
Haka kuma abin jira a gani shi ne ko Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, zai kai ga shiga filin zaben shugabancin Najeriya a kakar zaben 2023, ko shi ma zai karbi Awalaja kamar yadda magoya bayansa su ke zargin Shekarau ya yi? Lokaci ne zai tabbatar da haka!