• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

byRabilu Sanusi Bena
4 months ago
Fim

Shafin Rumbun Nishadi shafi ne daya saba zakulo muku fitattun jaruman kannywood har ma da masu tasowa, inda a yau shafin yayi cozali da daya daga cikin fitattun jaruman Tiktok wanda yake taka rawa a yanzu ta bangaren barkwanci, kuma daya daga cikin jaruman Kannywood masu tasowa, wato ABDUL’AZIZ SALISU wanda aka fi sani da D MALAM DAN BOLA.

Matashin Jarumin ya bayyana wa masu karatu babban dalilin da ya ja hankalinsa har ya tsunduma cikin yin bidiyon barkawanci, da kuma shigarsa cikin masana’antar Kannywood, baya ga haka ya bayyana batutuwa masu yawan gaske wadanda suka shafi rayuwarsa da kuma sana’arsa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar mu RABI’AT SIDI BALA kamar haka;

  • LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
  • Gasar Gajerun Labarun Soyayya Ta LEADERSHIP HAUSA 2025

Ka yi ‘comedy’ sun kai kamar guda nawa?

Na yi ‘comedy’ da yawa, ban san ma iya adadinsu ba dan suna da yawa, amma duk wanda ya sanni a ‘comedy’ ya fi sanina da ‘comedy’ Dan Bola, ko shi Dan Bola bidiyonsa ya kai saba’in da wani abu iya shi kadai kawai, karbuwarsu Alhamdulillahi mutane sun karbi Dan Bola, sai dai godiya ga Allah.

Ka yi shi ne kamar ‘series’ kenan?

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

Na yi shi kamar ‘series’ amma ba ‘series’ bane, ‘part-part’ ne na yi shi haka ba wani me tsayi bane ba, baya wuce minti uku zuwa biyar ya ma yi tsayi kenan.

Kai ka ke rubuta ‘comedy’ din ko kuwa bayar wa ka ke a rubuta maka?

Ni nake rubuta ‘comedy’ na da kaina, sai dai idan ana hira da abokai ana abun dariya haka da sauransu, sai in dauke shi, shi ma din ko da ban rubuta ba in yi shi akai, mu je mu yi bidiyon shi a duk lokacin da muka samu dama to, gaskiya ba a rubuta mun ‘comedy’ sai dai irin a ba ni ‘idea’ haka.

Ko akwai wani ‘comedy’ da ka taba yi wanda ya janyo maka zagi wajen mutane?

Ban taba bidiyon da ya jawo mun zagi a wajen mutane ba, sai dai kin san duk abin da ka ke dole akwai wanda ba fa burge shi ka ke yi ba, kuma mukan sanya number akan bidiyo haka nan wani zai bushi iska ya kira ka kawai ya kunduma maka zagi, ban sani ba ko shi samun nishadinsa ta nan yake samu, sai dai irin wadannan.

Wane irin nasarori ka samu game da wannan harkar ta comedy?

Nasarar dana samu nake jin dadi, nake alfahari da ita; mutane masoya ina jin dadi idan na ga yadda suke son bidiyoyi na, suke yabawa.

Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da ‘comedy’?

An sami kalubale sosai kwanan nan ma an samu, dake mun dan tafi hutun Dan Bola, sai na ce bari na dauko wani shiri na zo na ci gaba da saka wa kafin in dawo in cigaba da Dan Bola sai na dauko shiri mai suna Ango, muka saka ranar yin aiki muka dauko jarumai, da kyamarori da ‘light-light’ aka je aka fara wannan aiki ana tsaka da aiki kawai dai Aljanun Jarumar da take tsaka da yin aikin ya tashi, ba mu gama aikin ba aikin ya tashi, hankali kowa ya daga, darakta ya dan fara rukiya, a takaice dai sai da muka hakura da wannan aikin, aka kwashe aiki daga ‘computer’ washegari aka zo za a duba ‘sound’ babu kin ga ba aiki kenan, duk wata wahala da muka yi kama daga kan tattara jarumai, abincinsu, kudin sallamarsu, sannan kudin kayan aiki da muka dauko dukka haka muka yi asarar wannan aikin.

Na ji ka yi maganar jarumai, shin kana amfani da jaruman kannywood ne cikin ‘comedy’ ko kuwa Jaruman social media ne wadanda su ma suke baje hajarsu a kananun bidiyo?

Eh, na kan sanya jaruman kannywood a ‘comedy’ na, nayi comedy da Ali Nuhu, Na kowa, Bosho, Daushe.

Wacce hanya ka bi wajen ganin ka samu lokacin Ali Nuhu domin yin ‘comedy’, kuma ta ya ka sanar masa?

Muna da alaka da yallabai, dan shi yallabai maigida na ne a kannywood, saboda yana bibiyar lamura na akan abubuwan da na ke yi tun ma bamu taba haduwa da shi ba ya fara yi min ‘reposting’ a instagram, kuma yakan bani shawarwari idan ya ga ina yin wani abu da wanda bai kamata ba da kuma abun da ya kamata in yi. Allah cikin ikon sa har ya neme ni na je nayi fim din alaka, tun da har ya sa ni a alaka kin ga ai akwai alaka kenan, masha Allahu. Akwai lokacin da Arewa 24 suka gaiyace ni zasu yi interbiew da ni, suna gayyata na ke sanar masa Arewa24 za su yi hira da ni ya ce masha Allah Allah ya taimaka. Lokacin yayi naje su kayi interbiew da ni, bayan sunyi interbiew da ni, sai na kirawo yallabai na gaya masa na zo mun yi hira daArewa24 mun gama, sai nace sir kana office in kawo ziyara? ya ce yana ofis

Idan za ka yi ‘comedy’ kana kashe kudi kamar naira nawa wajen hada aikin?

Ya danganta da yanayin ‘comedy’ din da za ka yi, idan na tashi zan yi aiki bana fita nayi daya ko biyu, na kan rubuta kamar guda goma sai na fita nayi su, to kuma guda goman nan a kalla indai ina so na dan yi shi ‘normal-normal’ zan iya kashe talatin, arba’in haka, tunda kayan aikin na rana daya zan dauka.

A yanzu kana da mutanen da suke karkashinka za su yi kamar guda nawa?

A halin yanzu ban da wanda suke karkashi na sai dai abokaina, wanda tare ake tashi ayi gwagwarmaya.

Su waye abokanan aikin?

Abokanan ‘comedy’ na yawanci mata ne akwai wata yarinya mai suna Salma, akwai wani abokina yana nan shi ma muna fafata bidiyoyin shi Sani Mijin Biza, cikin sabon salon ‘comedy’ karya Da Gaskiya, da dai sauransu.

Wane abu ne ya fi baka wahala wajen yin ‘comedy’ ?

Abin da yake ban wahala shi ne; yarinya da za ka yi ‘comedy’ da ita babu abun a tattare da ita, ko ba ta rike ‘dialogue’ ko tana da saurin dariya, ina shan wahala da wannan abun.

Wane bidiyo ne ya fi burge ka cikin wanda ka yi?

Bidiyon da ya fi burge ni shi ne bidiyon Dan Bola, bidiyo na farko, wanda shi ne ya sa aka fara gani na, wanda na tawo ina tura bola ina cewa; “Za a kwashe bola?” kawai sai na ga budurwa ta, na duke na ce “Kai ina! karya ne ke wallahi Bebi ni ne” ina son wannan ‘comedy’ sosai.

Idan aka ce ka dauki daya ‘comedy’ ko fim wanne za ka dauka?

Fim zan zaba, ai fim baban ‘comedy’ ne, shi ya haifi ‘comedy’, na fara ‘comedy’ ne sakamakon ina son na kai ga fim.

Bayan wannan harkar taka da ka ke yi kana yin wata sana’ar ne?

Eh! Ina yin harkar ‘Gold’ kamar su zoben zinare, da Agogon zinare, sannan kuma da sauran ma’adanai, kamar su; ‘Blackstone’, ‘Tender stone’, da su jigida na ‘gold’ da sauransu.

Mene ne burinka a nan gaba game da bidiyon da ka ke yi da kuma harkar fim?

Burina shi ne na shahara nayi sunan da duk duniya za ta sanni kuma ta yi alfahari da ni, kuma na bada gudunmawa a addini na addinin musulunci

Wacce shawara za ka bawa masu irin sana’arka ta ‘comedy’?

Shawarar da zan ba su su tsaya su lura su yi abu mai kyau, kar su tsaya iya nishadi koyaya ne su rika sanya abu mai ma’ana tare da sako, domin an ce in yau kai ne- gobe ba kai bane, sabida haka a guji sanya kalaman batsa domin hakan ba shi da kyau.

Ko kana da wadanda za ka gaisar?

Ina gaishe da baban ogana wanda nake alfahari da shi a masana’antar kannywood wato Isma’il Maigana, darakto dan shi yake ba ni umarni akan bidiyoyi na, sannan ga abokina abokin gwagwarmaya Sani Mijin Biza, sannan akwai Adam A Beach, kuma akwai abokina wato Shafi’u Nadir Dan So.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
Nishadi

An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana

October 4, 2025
Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa
Nishadi

Daga Kallon Fina-finan Indiya Na Samu Sha’awar Fadawa Kannywood – Kamalu Mijinyawa

September 28, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran

Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version