Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira biliyan 486.218 a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Litinin.
A cewar Gwamnan, a lokacin da yake gabatar da kasafin mai taken “Budget of Service” ga majalisar dokokin jihar ya ce kasafin kudin da ake shirin yi ya nuna karin kashi dari bisa dari idan aka kwatanta da kasafin kudin shekarar 2024.
Finitiri ya ce daga cikin kasafin kudi na naira biliyan 486 na kudaden da ake kashewa a kai a kai za su kai naira biliyan 137, wato kashi 28.23%, ragowar Naira biliyan 348, wato kashi 71.77%, za a kashesu ga manyan ayyuka.
Ya ce gwamnatinsa ta yi alkawarin cimma manufofinta guda takwas, wato tsaro, samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, wadatar abinci, da ilimi a cikin wannan kasafin kudin 2025.
Gwamna Fintiri ya ce an kuma ware kasafin Naira biliyan 88 domin gina tituna a fadin jihar, ya bayyana kudirin gwamnatin na inganta hanyoyin sufurin kayayyaki a jihar.
“Muna sa ne da muhimmancin da ya wajaba a kanmu na hada garuruwa da hanyoyin mota domin saukaka wa da fadada tattalin arzikinmu cikin gaggawa,” in ji shi.
Majalisar karkashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon Bathiya Wesley, tun daga lokacin ta karanto kudirin dokar a karo na 2 kuma ta mika kudurin kasafin ga kwamitin kudi, da kasafin kudi domin tantancewa.
Karatu na biyu ya biyo bayan kudirin da shugaban masu rinjaye Hon. Kate Raymond Mamuno (Mazabar Demsa) da Hon. Musa Mahmud Kallamu (Mayo Belwa).
Da yake jawabi a takaice gabatar da kasafin kudin, shugaban majalisar Rt. Hon Bathiya Wesley, ta yabawa gwamnan bisa nasarar gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.
Haka kuma ya bada tabbacin shirye shiryen majalisar karkashin jagorancinsa na yin duk abin da ya dace domin ganin an gaggauta zartar da kasafin kudin da ake son aiwatarwa a shekarar 2025.