Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya sanar da bada tallafin dubu 10, ga kowane matashi ɗan bautar ƙasa duk wata a jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Talata a sansanin matasa masu yi wa kasa hidima da ke Damare a karamar hukumar Girei, lokacin bikin rantsar da matasan rukunin C na 2023, su 1340, da aka tura jihar.
- Gwamnati Ta Amince A Kashe Naira Biliyan N110 Don Gina Tituna A Fadin Nijeriya
- Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi
Ya ce haka ita ce manufar gwamnatinsa na yin alfarma da kyautatawa mutane, da nufin rage radadin da cire tallafin man fetur ga matasa.
Haka kuma gwamnan ya ba da tallafin man girki jarka 10, buhunan shinkafa 50, shanu 10 ga matasan.
Gwamna Fintiri, ya kuma taya matasan murnan kammala karatun da suka yi a makarantu daban-daban, wanda ya bayyana da cewa zai taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai.
Da yake magana a bikin ko’odinetan hukumar NYSC a jihar, Jingi Denis, ya bayyana zaman lafiya da cewa ya inganta a jihar, ya ce mafiya yawan matasan hukumar za ta turasu kananan hukumomin jihar ne.
Mista Jingi Daniel, ya yi rokon da gwamnatin jihar ta fadada kudaden tallafin da ta ke bai wa matasan da ke karkashin hukumar ilimin Firamare ta jihar zuwa ga sauran makarantun gwamnatin baki daya.