Firaministan kasar Dominica Roosevelt Skerrit ya kai ziyara a kasar Sin tun daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Maris. A yayin ziyararsa, ya yi hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Dominica da Sin, Sin ta fahimci damuwar kasar Dominica kan sauyin yanayi a matsayin wata kasa da ke karamin tsibiri, kuma tana son samun bunkasuwar tattalin arziki mai ‘yanci kai a matsayin kasa mai tasowa.
Skerrit ya kara da cewa, raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ya kawo damar samun bunkasuwa ga kasar Dominica da sauran kasashe, kasar Dominica ta nuna goyon baya ga tunani da kiran kasar Sin, kana tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen bin ra’ayin bangarori daban daban da sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya baki daya.
Hakazalika, Skerrit ya jaddada cewa, kasar Dominica ta nuna goyon baya ga ka’idar “Sin daya tak duniya”, wadda take bin dokokin kasa da kasa. Idan aka girmama dokokin kasa da kasa, to tilas ne a girmama ka’idar. Wannan ba sa da nasaba da tsarin kasa, ya kamata MDD da dukkan kungiyoyin kasa da kasa su nuna goyon baya ga dokokin kasa da kasa. (Zainab Zhang)