Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana cewa, kasar ta kimtsa tsaf wajen yin aiki tare da kasar Habasha domin karfafa ci gaban aikin layin dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, wanda yake muhimmin aikin hadin gwiwa mai inganci na kawancen “ziri daya da hanya daya” (BRI), da kuma fadada harkokin cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.
Li ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi yayin ganawarsa da firaministan Habasha, Abiy Ahmed a Rio De Janeiro, fadar mulkin kasar Brazil.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Ga Membobin BRICS Da Su Zamo Ginshikan Bunkasa Sauyi Ga Tsarin Jagorancin Duniya
- Xi Ya Ba Da Amsar Wasikar Matasan Amurka ’Yan Wasan Kwallon Pickle Bisa Ziyartar Sin
Li ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron ministocin dake bibiyar aiwatar da matakan da aka dauka a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) na watan Yuni, inda ya bayyana sabbin matakai masu muhimmanci, kamar aiwatar da tsarin soke harajin shigar da kaya kasar Sin da kashi 100 bisa 100 ga kasashen Afirka 53 masu huldar jakadanci da kasar.
Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki sabbin matakai a matsayin damammakin yin aiki tare da kasar Habasha domin samun cikakkiyar nasarar abubuwan da aka cimma a taron kolin Beijing na FOCAC.
Firaministan na kasar Sin ya kuma yi kiran kara zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, da mai da dangantakar da ke tsakaninsu ta zama abar koyi don gina al’ummar Sin da Afirka mai mako ta bai-daya a dukkan fannoni domin sabon zamani.
A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa.
Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp