A jiya Juma’a ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar don yin nazari da sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin dandalin hada-hada ta kafar intanet.
Taron ya yi nuni da cewa, bunkasuwar tattalin arzikin dandalin hada-hada ta kafar intanet na da matukar muhimmanci wajen fadada bukatun cikin gida, da tabbatar da daidaiton ayyukan yi, da tabbatar da zaman rayuwar jama’a, da samar da sabbin karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare
- ’Yan Bindiga Sun Sace ’Yan Uwan Ɗan Jarida a Kogi, Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 50
Ya kuma yi kira da a yi kokari wajen karfafa tsarin dandalin intanet na masana’antu, da tallafa wa dandalin kamfanonin intanet na sayar da kayayyaki don cin gajiyar damar da ke akwai a kasuwanni da inganta tsarin bin doka da oda kan yadda bayanai ke tafiya tsakanin iyakokin kasa da kasa.
Taron ya kuma tattauna wani daftarin doka kan amincin sinadarai masu hadari, tare da amincewa da daftarin shawarar yin kwaskwarima da soke wasu ka’idojin gudanarwa. (Mohammed Yahaya)