ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yan Bindiga Sun Sace ’Yan Uwan Ɗan Jarida a Kogi, Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 50

by Abubakar Sulaiman
2 years ago
Bindiga

Rundunar ’Yansandan Jihar Kogi ta tabbatar da sace ’yan uwa uku na tsohon Editan Daily Trust, Malam Ahmed Ajobe, ciki har da ƙanwarsa, Halimtu-Sadiya Tahir.

An sace su ne a ranar Alhamis a hanyar Ankpa-Adoka-Makurdi da ke cikin ƙaramar hukumar Ankpa, yayin da suke dawowa daga kasuwa a wani ƙauye kusa da Awo.

  • Manomanmu Sun Tabka Asarar Sama Da Naira Miliyan 100 A Harin ‘Yan Bindiga – Dan Majalisa
  • ‘Yan Bindiga Sun Kone Gonakin Manoma A Zamfara

Kakakin ’Yansandan Jihar Kogi, William Aya, ya bayyana cewa DPO na yankin ya tura jami’ansa don ceto waɗanda aka sace. Haka kuma, Kwamishinan ’Yamsanda, Bethrand Onuoha, ya umarci tawagar ’yansanda na musamman da su ƙarfafa aikin ceto a yankin. Aya ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa don ganin an Kuɓutar da waɗanda aka sace tare da gurfanar da masu laifin a gaban shari’a.

ADVERTISEMENT

Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi fansar Naira miliyan 50 don sakin su. Wani ɗan uwansu, wanda ya zabi a sakaye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne yayin da waɗanda aka sace suka je kasuwa domin siyan kayan shirin addu’ar kwana bakwai na mahaifiyar Ajobe, Malama Aishetu Tahir, wadda ta rasu a ranar Lahadi sakamakon rashin lafiya.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu babu wani kuɗin fansa da aka biya, kuma waɗanda aka sace suna can.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi

2027: DSS Ta Kama Waɗanda Ake Zargi Da Shirin Kai Hari Kan Ma’aikatan INEC

Bindiga
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu
  • Abubakar Sulaiman
    Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama
  • Abubakar Sulaiman
    Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

MASU ALAKA

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar
Tsaro

’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi

October 21, 2026
INEC Ta Ba Jam’iyyu Wa’adin 24 Ga Oktoba Kan ’Yan Takarar Da Aka Cire A Sunayen Da Ta Fitar
Tsaro

2027: DSS Ta Kama Waɗanda Ake Zargi Da Shirin Kai Hari Kan Ma’aikatan INEC

October 21, 2026
Hafsan Sojoji Ya Ziyarci Borno Yayin Da Ɗalibai 78 Ke Cika Kwanaki 155 A Hannun Masu Garkuwa
Tsaro

Hafsan Sojoji Ya Ziyarci Borno Yayin Da Ɗalibai 78 Ke Cika Kwanaki 155 A Hannun Masu Garkuwa

October 18, 2026
Next Post
 ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare

 ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026
Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

October 24, 2026
Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

October 24, 2026
Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

October 24, 2026
MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

October 24, 2026
Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

October 24, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.