Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aike da sakon taya takwaransa na Sao Tome da Principe Patrice Trovoada, murnar kama aiki a matsayin firaminista.
Cikin sakon nasa, Li Keqiang ya ce tun bayan dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasashen 2, Sin da Sao Tome da Principe sun ci gaba da bunkasa dangantakarsu yadda ya kamata, tare da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da fadada hadin gwiwar cin moriyar juna, wanda ke amfanar al’ummun sassan 2.
Li ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmancin gaske kan bunkasa huldarta da Sao Tome da Principe, kuma a shirye take ta yi aiki tare da ita, wajen ingiza sabon ci gaban cikakkiyar hadin gwiwa, da za ta samar da alhanu mai dimbin yawa ga kasashen, da al’ummun su baki daya. (Saminu Alhassan)