Bisa gayyatar da gwamnatin jamhuriyar Indiya ta yi masa, firaministan kasar Sin Li Qiang zai halarci taron kolin kungiyar G20 karo na 18 da za a gudanar a birnin New Delhi na kasar Indiya a ranakun 9 da 10 ga watan Satumba, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta sanar a yau Litinin. (Yahaya)
Talla