Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.
Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)