Gwamnan jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang ya ziyarci al’ummar Zikke da Kimakpa a karamar hukumar Bassa domin jajanta wa wadanda harin ta’addanci ya rutsa da su da ya yi sanadiyar rayuka sama da 50.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Mutfwang ya bayyana matukar alhininsa kan lamarin, inda ya ce duk da kokarin da gwamnati ta yi, gwamnatin ta gaza wajen dakile afkuwar lamarin.
- Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”
- Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – Ndume
A cewarsa, “Al’ummar kasa gaba daya suna makoki tare da ku, kasashen duniya suna makoki tare da ku, na ta yin kuka tun jiya (Litinin),” in ji gwamnan cikin tausayawa.
Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.
Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp