Firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin Pakistan da Sin a matsayin wadda ba za ta wargaje ba. Yana mai bayyana fatan ganin ziyararsa a kasar Sin, ta taimakawa kasashen biyu wajen kara zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.
Firaminista Shahbaz ya bayyana haka ne kwanan nan yayin hira da manema labarai na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, gabanin ziyararsa a kasar Sin.
Ya kara da cewa, kasar Pakistan tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya. Kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba zai iya ballewa ba. Yana mai cewa wannan ya kasance manufar da gwamnatin Pakistan ke bi a ko da yaushe. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp