Firaministan Serbia Milos Vucevic, ya ce ta hanyar hadin gwiwa da Sin, Serbia ta samu nasarori a bangaren sufurin jiragen kasa. Ya ce kasar ta saye sabbin jirage 5 daga Sin, kuma nan ba da dadewa ba za a kaddamar da layin dogo mai saurin tafiya tsakanin babban birnin kasar Belgrade da iyakar kasar da Hungary dake yankin arewaci.
Milos Vucevic ya bayyana haka ne yayin hirar da ya yi da wakilin CMG a baya-bayan nan, inda ya ce karkashin hadin gwiwar Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da ayyuka da dama na ginin ababen more rayuwa a Serbia. A cewarsa, wadannan ayyuka sun samar da ci gaba a fadin kasar tare da inganta rayuwar al’ummar kasar.
Ya kara da cewa, dukkan jarin sun bayar da gudunmuwa ga karuwar alkaluman GDP da ma daukacin tattalin arzikin kasar, wanda ya kai ga karuwar albashi da kudin pansho. Ya ce wannan ci gaba ya shafi kowanne bangare, shi ya sa Serbia za ta ci gaba da hadin gwiwa da Sin kan sabbin ayyuka. (Fa’iza Mustapha)