Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, yin adalci kamar yadda ya kamata shi ne muhimmin abu mai daraja a wurin kasashen duniya.
Li ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron muhawara na babban taron MDD karo na 80.
Li ya jaddada cewa, a matsayinta na mambar da aka kirkiro MDD tare da ita, kasar Sin ta taka rawar gani sosai a harkokin duniya, kuma ta yi aiki tukuru domin kyautata rayuwar bil’adama.
A shekarun da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani kudiri na hangen nesa game da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama, da kuma shawarar raya ci gaban duniya, da shirin samar da tsaro na duniya, da shirin bunkasa wayewar kai a duniya, da shawarar inganta jagorancin duniya (GGI), domin bayar da gudunmawar hikimomin kasar Sin da samar da mafita wajen kawo sauye-sauye a duniya, da shawo kan dimbin kalubale masu cin tuwo a kwarya.
Ya yi alkawarin cewa, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da dukkan bangarori, wajen daukar matakai madaidaita masu inganci, don warware wasu matsaloli da ake fama da su da kuma karfafa zaman lafiya da ci gaban duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp