Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bukaci taron koli na kasashen yankin gabashin Asiya, da ya tsaya tsayin daka kan rawar da yake takawa, ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa da dauwamammen bunkasuwa a yankin, yayin da ake fuskantar sabon yanayi da kalubale.
Da yake jawabi a yayin taron da aka gudanar a birnin Jakarta na kasar Indonesiya, Li ya ce yankin gabashin Asiya na da cikakkiyar masaniya kan matsalolin ci gaba da ake fuskanta, da wajibcin bude kofa, da muhimmancin zaman lafiya. Ya kara da cewa, yankin ya kuma fahimci cewa, hadin kai yana nufin samun wadata, kuma rarrabuwar kawuna babu abin da zai haifar sai koma baya.
Da yake maraba da dukkan bangarorin da za a dama da su a dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku, Li ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufar bude kofa ga kasashen waje, kana za ta ci gaba da raba damarmakin samun ci gaba tare da dukkan kasashe.
Yayin ganawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres a birnin Jakarta, a wannan rana kuwa, firaminista Li Qiang ya bukaci al’ummomin kasa da kasa, da su yi taka tsan-tsan kan batun basussukan da ake bin kasashe masu tasowa bisa tsarin aikin hadin gwiwa da kuma raba nauyi bisa adalci. (Ibrahim Yaya)