A Talatar nan ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da sakatariyar cinikayyar Amurka Gina Raimondo a birnin Beijing, inda ya yi kira ga Sin da Amurka da su inganta hadin gwiwar cimma moriyar juna.
Li Qiang, ya ce Sin ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da Amurka ke matsayin kasa mai ci gaba mafi girma a duniya, don haka ya dace sassan biyu, su karfafa hadin gwiwar su domin cimma moriya tare, su rage sabani da fito na fito, kana su hada karfi da karfe wajen bunkasa farfadowar tattalin arziki, da shawo kan kalubalolin dake addabar sassan kasa da kasa.
Kana mataimakin firaministan kasar He Lifeng, shi ma ya gana da sakatariyar cinikayyar Amurka Gina Raimondo a Beijing. Yayin ganawar ta su a Talatar nan, jami’an biyu sun zurfafa tattaunawa mai ma’ana, game da yadda za a aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka amince a taron Bali, da ma batutuwan tattalin arziki da na cinikayya dake jan hankulan kasashen 2.
Bangaren Sin dai ya bayyana damuwa, game da matakan da Amurka ke aiwatarwa, ciki har da sashe na 301 na dokar haraji, da hana wasu hajojin Amurka shiga kasar ta Sin, da kuma wasu matakai na dakile zuba jari da sassan biyu ke aiwatarwa ga juna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)