Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, babban abin da ya shafi alakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai shi ne hadin gwiwa, kuma dangantakar ta kasance ta samun moriyar juna.
A ganawarsa da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai, Uwar gida Ursula von der Leyen a gefen taron kolin kungiyar kasashen G20, Li ya bayyana cewa, Sin da Turai, a matsayinsu na manyan rukunoni biyu na duniya, kuma manyan injuna biyu na ci gaban duniya, kamata ya yi su kara kusantowa da juna. da kuma kara inganta hadin gwiwarsu. Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu, da su kawar da rashin tabbas dake faruwa a yanayin kasa da kasa tare da daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Turai.
A nata bangaren kuwa, Von der Leyen ta ce, tun daga farkon wannan shekara, mu’amala tsakanin kasashen Turai da Sin na ci gaba da karfafa, tare da samun sakamako mai kyau. Ta kara da cewa, bangaren Turai, yana son karfafa tattaunawa da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni daban daban, don tinkarar sauyin yanayi tare da sauran kalubalolin da duniya ke fama da su.
Bugu da kari, firaminista Li Qiang ya bayyana a yau cewa, ya kamata kasashen Sin da Birtaniya su yi watsi da yadda ake hada batutuwan kasuwanci da tattalin arziki da siyasa da tsaro, maimakon haka su inganta tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori da dama bisa jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya.
Li wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da takwaransa na Birtaniya Rishi Sunak a gefen taron G20, ya ce, kasashen Sin da Birtaniya dukkansu masu goyon baya ne, masu kwarewa kuma wadanda suka ci gajiyar cinikayya cikin ‘yanci.(Ibrahim)