A jiya ne, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya tattauna da takwaransa na kasar Singapore Lee Hsien Loong da ke ziyara a nan birnin Beijing,fadar mulkin kasar Sin inda sassa biyu suka sha alwashin ci gaba da yin hadin gwiwa.
Li ya bayyana cewa, a matsayin Lee na tsohon abokin da Sinawa suka saba da shi, kuma daya daga cikin rukunin farko na shugabannin ketare da ya tarba, tun bayan da ya zama firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin, wannan ya nuna cewa, kasashen Sin da Singapore, sun dora muhimmanci matuka kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce, yayin da kasashen Sin da Singapore ke tsayawa tsayin daka, wajen kare dunkulewar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar duniya daban-daban, a hannu guda kasarsa tana son hada kai da bangaren Singapore, don yin hadin gwiwa don nuna adawa da yunkurin siyasantar da batutuwan tattalin arziki, da wuce gona da iri kan batun tsaron kasa, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da tsarin tafiyar da harkokin masana’antu da samar da kayayyaki, da tabbatar da tsarin ciniki tsakanin sassa daban-daban, bisa jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya.
A nasa bangare Lee Hsien Loong ya lura da cewa, kasar Sin a matsayinta na daya daga cikin manyan abokan hadin gwiwar ASEAN, dukkan kasashen Asiya suna goyon bayan raya hulda da kasar Sin, kuma suna fatan karfafa hadin gwiwa tare da yin amfani da damar da kasar Sin ta samu, wajen farfado da tattalin arzikinta da kara bude kofarta ga kasashen waje bayan annobar COVID-19.
Ya kara da cewa, kasar Singapore tana maraba tare da goyon bayan kokarin kasar Sin, na shiga yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki na zamani da cikakkiyar yarjejeniyar abokantaka a tsakanin kasashen dake yankin tekun Pacific, kuma tana son hada kai tare da kasar Sin wajen tabbatar da tsarin ciniki na kasa da kasa bisa gaskiya, mai salon bude kofa. (Ibrahim)